Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

5 Oktoba 2023

13:59:24
1398143

An Yi Taron Gabatarwa Da Gungun Matasan Kasar Kenya Bayanai Na Ayyukan Majalisar Ahlul-Baiti (A.S.) Ta Duniya.

A wani taron hadin gwiwa da kungiyar matasan musulmin kasar Kenya, Wasu daga cikin jami'an majalisar Ahlul-Baiti (AS) sun bayyanawa matasan irin ayyukan wannan majalissar.

  Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, a wani taron hadin gwiwa da wasu jami’an majalisar Ahlul-baiti (AS) suka gudanar tare da wasu gungun matasa a cibiyar musulunci ta Jafari da ke babban birnin kasar Kenya, Dakta Mahdi Farmanian, mataimakin shugaban majalisar a fannin kimiya da al'adu na majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya gabatar da sassa daban-daban na wannan ofishi, musamman ma barayin babban daraktan kula da harkokin yanar gizo.

Application Nabaa, Rahnama portal, ɗakin karatu na dijital da Shia wiki suna daga cikin samfura da hanyoyin sadarwa da Dr. Farmanian ya gabatar wa matasan Kenya, kuma an ba su giga 40 na dijital da ke dauke da koyarwar Musulunci a cikin harsuna 36.

    Hujjatul-Islam “Waliullah Mandaripour” babban darektan kula da ilimi na majalisar kula da harkokin kimiya da al’adu na majalisar, shi ma ya bayyana a shirye ya ke na gudanar da kwasa-kwasan darussan da suka shafi fannoni daban-daban ta yanar gizo da kuma kaitsaye.

"Muhammed Kazem Kazemi", manajan cibiyar sadarwar tauraron dan adam ta Saqlain, shi ma ya bayyana cewa wannan cibiyar sadarwa tana aiki da harshen Larabci inda ya ce: Nau'oin samfuran kafofin watsa labaru da kuma kula da cibiyoyin sadarwar Saqlain sun kasance hanyoyin cigaba na sadarwar Saqlain na baya-bayan nan.

Hassan Sadraei Aref, shugaban kamfanin dillancin labarai na ABNA, yayin da yake magana kan ayyukan wannan kamfanin dillancin labarai a cikin harsuna 26, ya ce: Turanci, Swahili, Hausa da Faransanci, wadanda yawancin mutanen Afirka sun san wadannan yaruka, suna daga cikin harsunan ABNA. Kuma kokarin samar da Muhamman batutuwa na sadarwa masu dauke da yanayin ƙasa da ƙasa daga abokan aiki na gida da abokan aiki waje na ɗaya daga cikin mahimman manufofin ABNA a cikin sabon zagaye na ayyukanta.

A farkon wannan taro na karawa juna sani matasan Kenya, wadanda yawancinsu 'yan jarida ne da masu fafutuka a sararin samaniyar yanar gizo, sun bayyana ra'ayoyinsu kan wajibcin amfani da kafafen yada labarai da sararin samaniyar yanar gizo wajen yada ilimin addini.