Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

4 Oktoba 2023

11:15:45
1397784

Cin Zarafin Al-Qur'ani Ya Fi Karfin Ace Aiki Ne Na Wani Wawa Jahili.

Jagoran juyin juya halin Musulunci: Wasan Cacar Daidaita Alaka Da Gwamnatin Sahyoniya Karshen Asara Ce

Wajibi ne ga dukkanin shugabanni da masu rike da madafun iko na duniyar musulmi su yi tunani a kan muhimmin lamari na hadin kai da kuma sauran batutuwan da suka shafi wannan yanki wato laifuffukan da gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da aikatawa ya ce: A yau wannan tsarin Mulki ba wai daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran kadai yake kulle da cike da kiyayya ba jin haushi ba harma daga dukkan kasashen da suke kewaye da shi, kamar Masar da Sham kasar Iraki su ma suna ciki.

    Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, dangane da zagayowar ranar haihuwar Shugaba cika makon Annabawa, Muhammad Mustafa (AS) da kuma Imam Jafar Sadik (a.s) jagoran juyin juya halin Musulunci a kasa Iran ya gana da jami'an gwamnatin kasar da jakadun kasashen musulmi da bakin taron hadin kan Musulunci da kuma wata gungun jama'a daga bangarori daban-daban In da jagora ya bayyana hadarin da barazanar da azzalumai ke da shi ga koyarwar kur'ani mai tsarki a matsayin dalilin da ya sa suke shirya yin batanci ga wannan littafi na Ubangiji tare da jaddada cewa hanyar da za a bi wajen tunkarar tsoma bakin Amurka da azzalumai ita ce hada kan kasashen musulmi da kuma daukar manufa guda kan al'amurran yau da kullum, inda ya ce: cacar daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan kamar yin caca ne a kan dokin da aka tsere masa, tabbas za a yi asarar aiwatar da hakan, domin a yau gwagwarmaya Palastinu ta fi raye da kowane lokaci, kuma a shirye ta ke fiye da kowane lokaci, kuma gwamnatin masu kwace tana durkufewa tana mutuwa.

A cikin wannan taro, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya taya murna da murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (S.A.W) da kuma Imam Jafar Sadik (AS) tare da ganin cewa fahimtar dan Adam bata iya kaiwa ga fahimtar irin girman wannan mutum mai daraja, sannan harshen dan Adam kuwa ya gaza wsjen bayyana falalarsa ya ce: hasken Rana darajar annabi mai girma tana kan kafadar dukkan halittane kuma kowa bashi ne a gare shi domin annabi kamar kwararre kuma haziki likita ne mai ilimi da aiki da shi maganin duk wani babban ciwo kamar talauci, jahilci, zalunci, wariya, sha'awa, rashin imani, rashin manufa, fasadi na ɗabi'a da kuma kariya daga haifar da lalacewar zamantakewa ga ɗan adam.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da kimar ‘yancin rayuwa a wurin dukkan masu hankali na duniya a matsayin mafi girman hakkin dan’adam, ya kara da cewa: Allah yana cewa a cikin Alkur’ani cewa Annabi zai ba ku rayuwa ta har abada, wanda hakan zai tabbatar da farin cikinku a duniya da lahira, tare da cewa rayuwar ba mai karewa ba ce kuma ba mai cutarwa ba, don haka kowa daga cikinmu yana da hakkin Annabi akansa. Domin yana da hakkin rayuwa a kan bil'adama.

Jagoran juyin juya halin Musulunci bisa dogaro da ayar kur'ani mai tsarki ya kira hanyar biyan bashin ma'aiki "cikakkiyar jihadi a tafarkin Allah" yana mai cewa: Ma'anar jihadi ba wai jihadi da makami kadai ba ne, a'a jihadi daya dace a dukkan fagage, da suka hada da kimiyya, siyasa, ilimi da ladubba, kuma da jihadi a wadannan fagage, mutum zai iya biyan bashi ga wannan mai tsarki gwargwadon ikonsa.

Da yake jaddada cewa a yau kiyayya da Musulunci ta bayyana fiye da kowane lokaci, misali na irin wannan kiyayya cin mutuncin jahilci da akewa Alkur'ani,inda yiyi nuni da cewa: wawa jahili shike cin mutuncinsa gwamnati kuma ta goyi baya, wanda hakan ya nuna cewa al'amarin ya kasance kawai yunkuri ne cin mutunci ba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Ba ruwanmu da wannan jahili wanda ya ke yin wadannan ayyuka domin cimma burin wadanda ya fake da su, zai samu sakamakon hakan da kansa da mafi tsananin azaba ko kisa batu ake na masu tsara wadannan ayyuka ababen kyamata.

Ayatullah Khamenei ya dauki ra'ayin kaskanta Alkur'ani ta hanyar wadannan ayyuka a matsayin rudi, Kuma zai bayyanar da hakikanin fuskar makiya Alkur'ani nan kusa ya kuma kara da cewa: Alkur'ani littafi ne na hikima da ilimi da gina 'Dan Adam, farkawa, kuma kiyayya da Kur’ani a haƙiƙa ƙiyayya ce da waɗannan Fahimtar maɗaukakiya ne”. Tabbas Alkur'ani barazana ce ga gurbatattun kasashe domin kuwa ya yi Allah wadai da zalunci sannan kuma yana kushe mutanen da suka mika wuya ga azzalumai.

Ya dauki hujjar cin mutuncin Alkur'ani da da'awar da ake ta maimaitawa dangane da 'yancin fadin albarkacin baki ga masu da'awar hakan shi zai haifar da zubar mutumn masu riya hakan, inda ya ce: A kasashen da suka halasta cin mutuncin Alkur'ani da sunan 'yancin fadin albarkacin baki, shin su ma sun amince da cin mutuncin ga alamomin sahyoniyawa? Da wane harshe ne za mu iya tabbatar masu karara cewa suna ƙarƙashin mulkin azzalumai, masu aikata laifuffuka da wawure dukiyar duniya.

A wani bangare na jawabin nasa, yayin da yake ishara da zagayowar makon hadin kai, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi kira ga shugabanni da 'yan siyasa na kasashen musulmi da masana da masu fada a ji na duniyar musulmi da su yi tunani a kan tambayar da ke cewa, (Wane ne makiyin hadin kan kasashen musulmi kuma wa ke cutuwa da hadin kan musulmi ya kuma hana sanya dora hannunsu da wawure da tsoma bakinsu?)

Yayin da yake jaddada cewa hadin kan kasashen musulmi na yammacin Asiya da arewacin Afirka zai hana sata, tilastawa, da tsoma bakin Amurka, inda ya ce: A yau, Amurka tana kai hari kan kasashen yankin a siyasance da tattalin arziki, tana satar man fetur na kasar Syria, sannan kuma tana kara kaimi wajen ganin Yan ta'addan ISIS azzalumai, dabbobi, Mashaya jini, ta ba su kariya da ajiye su a sansanonin su don sake dawo da su fili a ranar bukata ta tsoma baki cikin lamuran kasashe, amma idan muka hada kai da Iran, Iraq, Syria, Lebanon , Saudiyya, Masar, Jordan da kuma kasashen yankin Gulf na Farisa suna da manufa guda daya tak a cikin al'amura na gava daya da na yau da kullum, masu tilastawa ba za su iya kuma ba su kuskura su tsoma baki cikin harkokinsu na cikin gida da na ketare ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Kamar yadda muka sha fada ba mu kwadaitar da wani yayi yaki da daukar matakin soji ba, haka nan kuma muna kaucewa hakan, don haka gayyatar da aka yi a hada kai da juna ita ce hana Aukuwar wutar yaki da Amurka ke yi, domin su ne suke fara kirkirar aukuwar yaki, sanadin duk yaƙe-yaƙen yankin yana daga kasashen waje ne.

Ya ce ya zama wajibi ga dukkanin shuwagabannin kasashen musulmi da su yi tunani kan muhimmin al'amari na hadin kai, da kuma sauran batutuwan yankin, wato laifuffukan da gwamnatin sahyoniyawa ci gaba da aikatawa yana mai cewa: A yau wannan gwamnatin ta Yahudawa ba wai tana cike da kiyayya ne da jin haushin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kawai ba harma tanajin hakan daga dukkan kasashen da suke kewaye da ita, kamar Masar da Siriya da Iraki.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira dalilin wannan kiyayya da jin haushi da cewa shi ne kin amincewar kasashe a lokuta daban-daban wajen cimma manufarsu, wato kwace kogin Nilu zuwa Kogin Furat, ya kuma kara da cewa: Suna cike da kiyayya da fushi ne ba shakka kamar yadda lafazin Alkur’ani mai girma da ke cewa: “Ku yi fushi ku mutu da wannan fushin.” Suna a halin mutuwa ne kuma da taimakon Allah wannan ayar da ta yi magana akan gwamnatin ‘yan kwace zata tabbata.

Ya kira batun Palastinu da kwace da korar al'umma daga gidajensu da azabtarwa da kashe su a matsayin Matsala ta farko a duniyar Musulunci a cikin 'yan shekarun da suka gabata yana mai jaddada cewa: tabbataccen yankakken ra'ayin Jamhuriyar Musulunci shi ne cewa gwamnatocin da suke dauki wajen cacar daidaita dangantaka da gwamnatin Sahayoniya a matsayin za su yi asara saboda wannan tsarin yana kan wucewa ne kuma kamar suna yin caca akan dokin da ya gaza.

Ayatullah Khamenei ya dauki matasan Palastinu da kungiyoyin gwagwarmayar da suke fuskantar cin zarafi da zalunci na Palastinu a matsayin mafi raye da kuzari kuma tana shirye fiye da kowane lokaci yana mai cewa: In sha Allahu wannan yunkuri zai tabbata, kuma Imam ya furta cewa gwamnatin mamaya tana a matsayin ciwon daji, wannan tsarin mulki ta hannun al'ummar Palasdinu da dakarun gwagwarmaya ne za su kawar da a yankin baki daya.


A karshe ya bayyana fatansa na cewa da yardar Allah al'ummar musulmi za su iya yin amfani da iyakoki na musamman na dabi'a da na dan Adam tare da alfahari da daukaka.


A farkon wannan taro, shugaban kasa Raisi a cikin jawabinsa, ya yi ishara da kokarin da Manzon Allah (S.A.W) yake yi na gina mutum da al'umma bisa "Tauhidi" da "Adalci" da gwagwarmaya wajen fuskantar da kuma tsayin daka a kan hanyar da za a bi wajen ganin an cimma nasara ga hadafin da aka jera a matsayin daya daga cikin muhimman koyarwar manzon Allah mai girma da daukaka, ya ce: hadewar duniyar musulmi bisa akidar hadin kai da gwagwarmaya da kore kafirci da sasantawa zai yi samar da wani sabon wayewar Musulunci.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da bullar bayyanar taimako da shiryarwa daga Ubangiji a cikin kwarewar juyin juya halin Musulunci na Iran, dogaro da Allah da kuma dogaro da al'umma da cin gajiyar fa'idar da ake samu a duniyar musulmi, ya yi la'akari da abubuwan ci gaba da samun ci gaban nasara kan masu son zuciya. inda ya kara da cewa: sulhuntawar wasu gwamnatoci da gwamnatin sahyoniyawan ba za su zama masu samar masu da tsaro ba saboda wannan gwamnatin tana kan rushewa ne, kuma nasarar gwagwarmayar tana nan kusa.