Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

3 Oktoba 2023

20:53:51
1397655

Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Gana Da Wakilan 'Yan'uwa Na Harka Islamiyya A Gidansa Da Ke Abuja.

Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Gana Da Wakilan 'Yan'uwa Na Harka Islamiyya A Gidansa Da Ke Abuja.

  Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A cikin jawabin Jagora (H) bayan tattauna batutuwa da dama, ya bayyana cewa; sakon Manzon Allah (S) shi ne cikar sakon dukkan Annabawa da Manzanni. Hanyar isar da sakon Annabawa ya bambanta, shi Manzon Allah da hikima ya zo, wanda shi ne Alkur'ani. Sai ya zama alummar zamanin Annabi (S) sun kasa kawo abin da ya yi kama da Alkur'ani. Alkur'ani ya zama sakon da yake kunshe cikinsa ya saba da dukkan wani abu da aka sani a baya.

Manzon Allah mutum ne, amma fa ba kamar sauran mutane bane, hatta a halittarsa. Masu gaba da Ahlul Baiti ne suka kirkiro hadisan da ke nuna Annabi (S) mutum ne addi (mutum kamar kowa). Kuma sun yi hakan ne domin su tauye darajar Manzon Allah (S), cewa Annabi bai iya karatu da rubutu ba cin mutunci ne ga janibin Annabi (S). A wurinmu Annabi tun ranar da aka haifeshi Annabi ne shi, izini ne ba a mishi ba ya isar da sako sai da ya cika shekara 40 a duniya.

17/Rabi'ul Awwal/1445

02/10/2023