Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

3 Oktoba 2023

18:13:42
1397633

SUNAN MU MUSULMI KUMA ADDININ MU MUSULUNCI

Inji Shaikh Ibraheem Zakzaky a jawabin ranar Mauludin Manzon Allah (S) na bana (17/3/1445H)

 Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - Yace: “Sakon Hadin kai, ba a Makon Hadin Kai ne kawai ake yi ba, a ko wane lokaci, in mutum yana bibiyan zantukanmu, zai ga cewa muna ta kokari ne kan nuna cewa al'ummar Musulmi muke magana da su gabadayansu, muna kuma magana kan sakon Musulunci shi kansa. 

“Ba rarraba ya dame mu ba, ba muna cewa mu 'yan kaza ba ne. Ala bashi wasu su yi ta ce mana 'yan kaza, su basu damu ba, duk abin da muke fada kawai babu ruwansu kawai sunanmu 'yan kaza. To ko me kuka ga dama, ku yi ta fadi, amma mu dai sunan mu Musulmi, sunan addinin mu Musulunci, kuma duk wanda ya shaida da La' ilaha Illallahu Muhammadur Rasulallah, dan uwanmu ne Musulmi. 

“Kuma muna fatan Allah Ta'ala Ya hada kan wannan al'umma. Allah Ta'ala Ya nuna mana lokacin da wannan addini zai zama shi ne bisa, birbishin komai. Ya zama kuma wannan al'umma martabanta da karfinta ya dawo, In sha Allahul Azeem."