Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

2 Satumba 2023

18:35:48
1390694

Mutane 19 Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Mota Kan Hanyarsu Ta Zuwa Karbala A Samirra

Mutane 19 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani karo da wasu motoci biyu suka yi a kan titin Samra-Kazamain.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Husain Derakhshan, shugaban cibiyar kula da ayyukan gaggawa na kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran, ya ce: "Abin takaici, mutane 19 ne suka mutu a wannan lamari, wadanda suka hada da Iraniyawa 12, da 'yan Afghanistan 4, da 'yan Iraki 3."

Sunayen wadanda suka jikkata a hatsarin da maziyartan Iraniyawa suka yi a kan hanyar Kazimain-Samarra sune kamar haka: 

  Wadanda suka jikkata a wannan lamari wadanda Iraniyawa 7 ne da kuma ‘yan Afghanistan 4, an fara kai su asibitin Shahr Balad da ke kasar Iraki, amma bayan ‘yan sa’o’i kadan aka maida su asibitin Kazimain.

Sunayen wadanda suka jikkata a wannan lamari sun hada da.

Mahbobeh Rezaei - Zahra Fathi - Ali Mirabian - Behjat Rezaei - Najiba Sarvi - Abolfazl Hosseini - Sahar Mirabian - Hossein Hamtian - Zainab Gholami - Safar Ali Zahir

Manajan hulda da jama'a na kungiyar agaji ta Red Crescent ya bayyana cewa, wadanda hadarin ya rutsa da su ya kamata a kai su Iran ta hanyar motar daukar marasa lafiya.