Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

29 Agusta 2023

14:34:09
1389826

Ankore Ministar Harkokin Wajen Kasar Libya Bayan Ganawar Sirri Da Eli Cohen

Firaministan kasar Libiya "Najla Al-Monghosh" ministar harkokin wajen kasar an kore ta daga majalisar ministocin kasar bayan wata ganawar sirri da ta yi da ministan harkokin wajen gwamnatin sahyoniyawan.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Hukumar tsaron cikin gida ta Labiya ta kuma ruwaito cewa an haramtawa Najla Al-Monghosh fita har sai an gudanar da bincike kan ganawarya da ministan harkokin wajen yahudawan sahyoniya. A lokaci guda kuma, wasu majiyoyi sun ruwaito cewa ministan harkokin wajen Libya ta gudu zuwa Turkiyya.

Ana ci gaba da zanga-zanga a Libya biyo bayan ganawar sirrin ministocin guda biyu da Firaministan Libiya ya dakatar da ministan harkokin wajensa bayan ta gana da takwararta ta Isra'ila inda hakan ke nuna Libya ba ta amince da Isra'ila ba, saboda Tripoli na goyon bayan Falasdinawa, kuma ganawar ta haifar da zanga-zangar dayawa a kasar ta nuna kin jinin faruwar hakan.

Ministan Isra'ila Eli Cohen ya bayyana ganawar da Najla al-Mangoush a matsayin "mataki na farko mai tarihi na kulla dangantaka da Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na kokarin kulla alaka ta kut da kut da kasashen Larabawa da na musulmi, kamar yadda akasan Libya da arzikin man fetur tayiyu wannan ganawar tana da alakar tattalin arziki ga haramtacciyar gwamnatin ta Isra'ila.

Baya ga dakatar da Mangoush, Firayim Minista Abdul Hamid Dbeibah ya kaddamar da bincike a kanta. Cohen ya ce ya gana da Mangoush a makon da ya gabata a gefen taron kolin da aka yi a birnin Rome kuma inda suka tattauna yuwuwar dangantakarsu.

Sanarwar ta kuma ce, huldar ba ta kunshi wata tattaunawa, yarjejeniya ko tuntuba ba, kuma ma'aikatar ta "sabunta cikakkiyar kin amincewa da daidaitawa da Isra'ila.

Bayan rahotannin taron ne zanga-zangar ta barke a Tripoli babban birnin kasar da wasu garuruwa. An toshe hanyoyi, an kona tayoyi, sannan masu zanga-zangar sun daga tutar Falasdinu.

Majalisar shugaban kasar da ke wakiltar larduna uku na Libya, ta ce ba bisa ka'ida ba ne daidaita alaka da