Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, tun a ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin kasar Iraki ta ba wa Maziyartan Iran kariyar tsaro na hanyoyin tun daga mashigar iyaka ta Khosrawi zuwa Bagadaza a hukumance, Tare da bada tsaro ga maziyartan da ke tafiya ta bas daga Kurdistan Iraki zuwa Karbala, a hukumance.
Baya ga jibge su a kan hanyar Diyala-Baghdad-Kirkuk-Baghdad, sojojin na Basij kuma suna cikin shirin ko-ta-kwana a cikin hamadar Hamreen da tsaunukan da ke tsakanin larduna uku na Diyala da Kirkuk da Salahuddin.
Za a ci gaba da gudanar da wadannan shirye-shiryen bada tsaro har zuwa karshen Taro Arba'in da kuma dawo da mqziyartan Iran zuwa kasarsu.
.................