Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

20 Agusta 2023

10:32:45
1388098

JAWABIN SHEKH IBRAHIM ZAKZAKY (H) GA MASU ZUWA TATTAKIN ARBA’IN 2023 / 1445 / ASALIN TATTAKIN ARBA’IN DIN IMAM HUSAINI (AS)

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A shekaran jiya Asabar 2 ga Safar 1445 (19/08/2023) Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da masu shirya tafiya zuwa Tattakin Arba’in din Imam Husaini (AS) a Karbala, inda ya mika sakonsa ga masu Tattakin Arba’in a Iraq da na gida Nijeriya. Abin da ke biye rubutaccen jawabin Jagoran ne. Cibiyar Wallafa ta rubuto muku.

“A’uzu Billahis-Samee’il Aleem, Minash-Shaidanil La’inir Rajeem. Bismillahir Rahamanir Raheem. Wasallallahu Ala Sayyidina wa Nabiyina wa Habibi Qulubana Abil Qasim Mustapha Muhammad wa ala alihit Dayyibinad Dahireenal Ma’asumin, siyama Baqiyatullahi fil Ard Sahibul Asr waz zaman Arwahuna lahu fidha.

Assalamu alaikum wa rahmatullahi Ta’ala wa barakatuhu.

MAKASUDIN HADUWARMU

Makasudin haduwar mu a nan shi ne kamar bankwana da ku, wanda kuka zo a matsayin wakilan dimbin ‘yan uwa wadanda za su tafi Tattakin Arba’in a Iraq daga Najaf zuwa Karbala a bana, wala’alla kuma da wasu wadanda za su samu wannan damar kuma su wuce ziyara zuwa Masshadin Imamu Ridha (AS) a Masshad kuma a lokaci guda. 

To, bara ma mun yi zama irin wannan, kuma har nake cewa ainihin, wannan abin da zan fada a nan shi ne kamar sakonmu kuma har wala yau a lokaci guda ga masu halartan Tattakin Arba’in, ba kawai a can Iraq (a Najaf zuwa Karbala) ba, har da ma wadanda za su yi Tattakin Arba’in din ko tarurrukan Arba’in a nan gida Nijeriya.

ASALIN TATTAKIN ARBA’IN DIN IMAM HUSAINI (AS)

To, shi Tattakin Arba’in ya yo asali ne tun shekarar farko na shahadar Abi Abdullah (AS). Arba’in din farko, wanda aka ce Jabir bin Abdullah al-Ansari (Radiyallahu Anhuma), shine farkon wanda ya kai ziyara na Arba’in. Ya dai kai ziyara ne, sai ya dace da ranar Arba’in a Karbala. 

Ya tafi daga Madina, sannan da ya je sai ya sauka a bakin kogin Furat, ya yi wanka ya sanya tufafi masu tsafta, sannan ya bulbula turare, sannan ya taka da kafa ba takalmi, yana tafiya a hankali, cikin natsuwa da kuma yana Azkar, har ya isa makwancin Abi Abdullah (AS), ya dora hannunsa, ya kira shi da karfi har sau uku. Sannan ya fashe da kuka yana cewa, ina kiran masoyi na san masoyi na ji, amma ba zan ji amsar sa ba. Da wadansu kalamai dai masu sosa rai, wadanda suna nan a muhallinsu, idan mutum ya karanta.

Ana cikin haka nan, sai suka hango duhun wadansu mutane suna dimfaro wurin. Sai yace da wani bawansa, jeka ka duba mana ka ga wadancan masu zuwan su wane ne? In mutanen Ibn Ziyad ne sai mu samu wurin da za mu fake (wato su bar wurin, su je su samu mafaka kenan, su buya daga wadannan mutane). Yace, idan kuma Maulaya wa Sayyidi ne, Imam Zainul Abidin (AS) to. 

To sai kuwa ta zama Imam Zainul Abidina ne ke tafe. Don lokacin da za a koma da su Madina, su suka bukaci a bi da su ta nan, duk da dai kasar Karbala daga Dimashq ba hanyar Madina take ba, an kara tafiya ne, amma su suka bukaci a yi musu haka nan, kuma aka yi musu haka nan din. Sai kuwa shi bawan nasa ya dawo yace masa, ai Maulana wa Sayyiduna Imam Zainul Abidin ne. Har (Jabir) yace masa, “Anta Hurru li wajhillah.” (kai ‘yantacce ne saboda Allah). Nan take ya ‘yanta shi saboda wannan albishir da ya yi masa. 

To, sai ga shi Imam Zainul Abidin da Sayyida Zainabul Kubra (SA) da sauran iyalan Annabi (S) sun zo wannan muhalli, to nan suka hadu da Jabir Bin Abdullah al-Ansari. Imam Zainul Abidin yana cewa, ya Jabir, nan ne aka kayar da mazajenmu, nan ne aka fille kawuka dinmu. Maganganu masu sosa rai, duk aka yi ta kuka, aka yi ta koke-koke. To muna cewa wannan shi ne Arba’in na farko.

TATTAKIN ARBA’IN KOYI NE DA SAHABIN MANZON ALLAH (S)

To har nake cewa, ga masu maganganu, su ce kamar ku… Ka san wasu mutane, duk abin da su wa wurinsu basu san shi ba, sunansa bidi’a. Sai mu ce to lallai idan ma kun ce baku san shi ba, saboda haka ku a wurinku bidi’a ake yi, to wanda suke yi su sun san abin da suke yi, sun kuma san dalilin da yasa suke yi. Yauwa. Saboda haka ba lallai ne ya zama ku kun san shi, ko kun yarda ba ma. Abin da ya kamata in kun ga mutane suna wani abu, maimakon ku hukumta su da irin naku hukuncin, sai ku tambaye su me yasa suke yi? In suka gaya muku hujjarsu, to ba lallai ku yarda da Hujjar ba, ko ku gamsu ba, sai ku yi musu uzuri, cewa su suna da hujja.

Nake cewa, lallai kam idan kai Sunni ne, kuma kai mai I’itiqadin cewa Sahabbai adilai ne, kuma “Bi’ayyuhum ihtadaita ihtadait,” to Falillahil Hamdu. Jabir Bin Abdullahil Ansari sahabi ne mahaifinsa ma sahabi ne, kuma gwaraza a sahabban. An san mahaifinsa shi ne fa Manzon Allah (S) ya sa shi a kan romat ranar Uhud, yace ko kun ga ana fyauce mu ne kar ku tashi daga nan. 

An tuna da wannan kissa din? Wanda daga baya da suka ga yaki ya kawo karshe, sai suka ce suje su debi ganima. Sai yace ai Manzon Allah (S) yace, kar mu bar nan koma me ke faruwa? Suka ce in ana yaki ba? To sai suka tafi. An ce kamar mutum 50 ne, shine shugabansu. Sai suka bar shi cikin mutum 12. Kuma Khalid bin Walid da ya zagayo duk gaba daya ya kashe su. Duk gaba dayansu ba wanda ya yi saura. To ciki har da shi Abdullah al-Ansari din, mahaifin Jabir.

Aka ce, lokacin Umaru Binil Khaddab in yana rabo, idan ya zo kan Jabir, sai ya bashi kaso biyu, saura kowa ma ya bashi kaso daya. To sai Abdullahi dan Umar yace, ya baba, naga kana ba wannan mutumin kaso biyu, ni kuwa kaso daya kake bani. Sai yace ai duk lokacin da na ganshi ina tunawa da lokacin da Babansa ya dake, kai kuma naka baban ya gudu. Don haka yake bashi kaso biyu, yana tunanin yadda babansa ya dake har ya yi shahada, shi kuwa baban Abdullahi din rannan ya danna a guje. To kaga wannan Quduwa (abin kwaikwayo) ne, ya zama Quduwa, babansa ma Quduwa. Ko ba a lura ba? 

JABIR BIN ABDULLAH DAN SAKON MANZON ALLAH (S) NE

Sannan kuma Jabir bin Abdullahil Ansari ya yi tsawon rai, ya yi zamani da Amirulmuminin (AS), ya yi zamani da Hasan da Husain (AS), ya yi zamani da Aliyu Binil Husaini (AS), sai a zamanin Ali Binil Husaini ne har ma ya ga haihuwar Imam Baqi (AS), har ma ya isar da sakon da Manzon Allah (S) ya aike shi izuwa Imam Baqir yana jariri. 

Don Manzon Allah (S) ya fada masa A’imma 12, yace masa kuma za ka ga na biyar dinsu mai suna Muhammad wanda za a ma lakabi da Baqir, in ka ganshi kace ina gaishe shi. To kuma har sai da aka haifi Imam Baqir, sannan yace masa isar da sakon da Manzon Allah ya aike ka. Sannan ya isar da sako din.

Na san ba su da wannan ruwayar su Ahlussunnah, amma muna da shi mu. Yace Manzon Allah yana isar maka da ‘Salam’ (gaisuwa). Sai yace “Wa’alaihis Salam.” Kuma lokacin Imam Baqir yana jariri, amma yace “Wa’alaihis Salam Ya Jabir.” Sannan Jabir yace, na riga na isar da sakon nan, saura in tafi. Kuma bai dade ba ya rasu. To kaga shi Quduwa ne. Ko ba a lura ba?

MUNA DA RUWAYOYI DAGA A’IMMA (AS) A KAN JUYAYIN DA MUKE YI

Sannan kuma har wala yau, mu muna da ruwaya daga Imam Hasan al-Askari (AS), wanda yace, alamomin Mumini guda biyar ne, daga cikinsu sai ya ambaci Ziyaratul Arba’in. Yana daga cikinsu, sauran guda hudun ba sai mun kawo su ba tunda ba muhallinsu ba ne. Ziyaratul Arba’in na daga cikin alamomin Mumini, kuma wannan ziyarar Arba’in din yake nufi.

To, kaga kenan idan ma mutum ya ga muna abu, shi ya shafa bai gani ba, sai mu ce to in ka tambaye mu, mu muna da hujjarmu. Sannan kuma duk koyarwar A’imma dinmu, muna da har da Nassin Ziyarar Arba’in, sananne ne. To kaga kenan Tattakin da ake yi, a wurinmu ba kirkirarren abu ba ne, ba kuma mu ne muka ga ya kamata mu yi sai muka yi ba, dama zaunanne ne a koyarwar da Iyalan gidan Annabi (S) suka yi mana.

IYALAN MANZON ALLAH (S) NE SUKA FARA ZAMAN JUYAYIN ASHURA

To kuma haka ma zaman Aza na Shahadar Abi Abdullahi (AS), wanda shi ma Imam Zainul Abidin (AS) a lokacin da Yazidu yace ya roki komai zai masa. Bayan da duk abubuwa suka sukurkuce masa, Yazidu ko gari ya shiga sai ya ji ana la’antarsa, duk abin ya dame shi, sai ya zama yana tunanin su iyalan gidan Annabi su koma Madina. Har ma dai ya yi wasu abubuwa yana tunanin kamar ko ya fita kunya ne? Ya dauko Kwando shaqe da zinarori wai ya kawo musu. Har Sayyida Zainab (SA) tace, yanzu ba za ka ji kunya ba Yazid? Ka kashe Husaini ka bamu kudi? Yace to ya zan yi? Zan dawo da shi ne? ya riga ya tafi. Tace to kwashe kudinka ba mu bukata.

To sannan sai yace da Imam Zainul Abidin (AS), duk abin da kake so ka fada. Duk bukatarka ka fada. To sai ya fada masa wasu bukatu kamar guda hudu; yace masa na farko za mu tsai da zaman majalisin Aza a nan fadarka. Sai yace, a nan fadana za a yi Majalisin Aza? Sai su kuma mutane suka ce ai kai ka yi masa alkawarin duk abin da ya tambaya za a masa. Sai yace, to shikenan a yi. Kaga sai aka yi zaman Aza a fadar Yazidu. To kagani, zaman Aza din zaunannen abu ne. 

Kuma da suka kamo hanya, duk inda suka je sai Sayyida Zainabul Kubra (SA) tai ta ba da labarin abin da ya faru da su. A yi ta koke-koke. Kaga ita ta assasa wannan zaman Ashura duk kwanakin nan, har ya dace da Arba’in din da suka je. Kuma aka koma Madina ma ya zama danye. Randa suka isa Madina danyen abu ya zama. Aka yi ta kuka kamar rannan ne ranar Shahadar. Ba wani gida a Madina face koke-koke ake yi a lokacin. To kaga wannan zaunannen abu ne mu a wurinmu.

Koyarwa wanda muka samu rubutacce kuma koyarwar A’imma (AS) daya bayan daya, cewa akan gansu in wannan watan ya kama su kan ta nuna alamar bakin ciki ne, ba za a gansu sun yi dariya ba har akalla kwana goman farko, da kuma zaman jaje har duk wadannan kwanuka din.

RANAR 1 GA SAFAR AKA SHIGA DA IYALAN ANNABI (S) DIMASHQ

To, sannan kuma, rana mai kamar ta jiya, ranar 1 ga wata, domin yau muna 2 ga watan Safar. Rana mai kamar ta jiya, rannan ne aka ce a ruwaya aka shiga da kan Imam Husaini (AS) Dimashq. Wani irin Masa’ib da aka gani rannan, yadda shi Yazidu ya ma tari kan ne kamar ana biki, sannan kuma da aka shiga da iyalan Manzon Allah jifansu aka rika yi da dabinaye, ana jefo su da duwatsu, har ma wasu saboda keta ma har wuta sun wurgo. 

To, haka nan aka je da su, kuma da irin abubuwan da suka gamu da a birnin Dimashq a wadannan kwanakin, kafin shi ya saduda ya ga cewa kuma yanzu yana neman yadda za a fita lafiya ne, har yace ana iya komawa da su. 

Kun ga kenan da zaman jaje da yin jaje din, da kum Khasatan ma ziyarar Arba’in zaunannen abu ne.

Za mu cigaba.

— Cibiyar Wallafa

www.cibiyarwallafa.org