Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

20 Agusta 2023

06:57:48
1388046

Nijar: Jami'an Tsaron Da Su Kai Juyin Mulki Zasu Bada Mulki Nan Da Shekaru Uku

Ba Neman Mulki Mu Ke Ba, Za Mu Tantance Tsarin Gwamnati Nan Da Shekaru Uku

Tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka da aka fi sani da ECOWAS karkashin jagorancin "Abdul Salam Abubakar" tsohon shugaban kasar Najeriya ta isa birnin Yamai domin ganawa da mahukuntan kasar da kuma tattauna hanyoyin diflomasiyya da za a bi don fita daga rikicin.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Wannan tawagar ta gana da hambararren shugaban kasar Nijar, "Mohammed Bazoum", a Yamai. Kungiyar ta ce ta kuma gana da "Janar Abdulrahman Tian" jagoran masu yunkurin juyin mulkin, domin cimma matsaya kan hanyoyin da za a bi dan fita daga yanayin da ake ciki.