Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

13 Agusta 2023

04:36:26
1386618

Yin Batanci Ga Saukakken Littafi Goyon Bayan Bata Ne Da Nufin Yakar Shiriya

Tattaunawa Tare Da Yin Nazari Kan Girman Laifin Tozarta Alkur'ani Mai Girma

A wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (AS) ABNA ya yi tare da masana, yayi bincike da nazari kan cin mutuncin kur’ani mai tsarki a wasu kasashen yammacin duniya. A cikin wani taro da aka gudanar kafar yanar gizo a cikin wannan tattaunawar, masana biyu daga Lebanon da Iraki sun bayyana ra'ayoyinsu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA: Kila buga littafin «آیات شیطانی» shi ne na farko kuma mafi shaharar mataki na cin zarafi a fagen kur’ani mai tsarki da littafan musulmi masu tsarki. Duk da cewa cin mutuncin kur'ani ya samo asali ne tun farkon shekarun Musulunci, amma masu da'awar 'yancin fadin albarkacin baki da kuma da yahudawan sahyoniyanci na duniya suka aiwatar da wannan aiki sau da yawa a cikin 'yan shekarun da suka gabata.


A ranar 11 ga Satumba, 2010, aniyar "Terry Jones", wani limamin Amurka, ya nufin kona kusan kwafin 3,000 na Kur'ani, wanda hakan ya haifar da zanga-zangar da ta hana wannan mummunna aiki nasa, amma a lokaci guda, a cikin wannan shekara, Amurkawa masu adawa da Musulunci sun yi kokarin kona Al-Qur'ani. Bayan shekara guda, Terry Jones ya kona kur’ani a wata cocin Florida kuma ya buga hotunansa. Wannan mataki na daya daga cikin ayyukan kona kur'ani na farko a cikin al'umma a wannan zamani da muke ciki, wanda ya janyo maida martani daga musulmi da mabiya sauran addinai.


A makwanni da kwanaki da suka gabata, cin mutuncin alfarmar kur’ani mai tsarki da kuma wurare masu tsarki na musulmi tare da goyon bayan wasu kasashen yammacin duniya, ya yi sanadiyyar fusata da zanga-zangar da har ta kai ga “Papa Francis” shi ma ya shiga sahun masu yin Allah-wadai da kona Al-Qur'ani tare da bayyana kim jininsa ga wannan aiki na dabbanci.


Duk da cewa cin mutuncin wurare masu tsarki yana cutar da zukatan al'ummar musulmin duniya, amma wannan cin mutuncin ya kasance kwarin gwiwa ga al'ummar musulmi wajen tsayawa tsayin daka a kan makiya addini tare da samun "hadin kai" tare da tsayawa tsayin daka wajen ganin daukakar addinin Musulunci. Kamar yadda da yawa daga cikin jagororin Musulunci kamar Marajio'in Taqlid ta Iran da Iraki, da cibiyoyin Musulunci na Shi'a da Sunna, da kuma da yawa daga cikin masu fada a ji na Shi'a da Sunna, da kuma musulmi da dama a sassa daban-daban na duniyar Musulunci, sun yi Allah wadai da wannan mataki da murya daya.


Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - ya yi nazari kan cin mutuncin kur'ani mai tsarki a baya-bayan nan a hirarsa da masana. A yanayi na taron gidan yanar gizo da aka gudanar tare da halartar masu bincike da masana daga kasashen Labanon da Iraki, Dr. Musa Al-Khalaf, mamba a majalisar malaman Sunna ta kasar Labanon, da Farfesa Mahdi Al-Kaabi, masanin addini da na kasar kuma Masanin harkokin siyasa a Iraki, sun bayyana ra'ayoyinsu.


A farkon wannan taron Musa Al-Khalaf ya yi ishara da girman wahayi na kur’ani mai tsarki inda ya karanta aya daga cikin suratul Hashr 

(لو انزلنا هذا القران على جبل لرايته خاشعا متصدعا من خشيه الله وتلك الامثال نضربها للناس لعلهم يتفكرون) 

In da ya yo bayanin girman Alkur'ani ya na mai cewa : “A cikin faxin Allah: “ Da Ace mun saukar da wannan Alqur’ani a kan wani dutse, haqiqa saboda tsoron Allah, da za ka gan shi ya kaskantance yana mai dagargajewa, muna buga wadannan misalai ga mutane domin su yi tunani” wanda wannan magana tana nuna girman littafin Alkur’ani mai girma.


Wannan kwararre kan lamurran addini ya kara da cewa: kasashen yamma na kokarin tunzura al'ummar musulmi ta hanyar kona kur'ani daga lokaci zuwa lokaci, karkashin dokar kasa da 'yan sanda. Wadannan ayyuka na kyama suna nuna irin girman kiyayyar addini a cikin zukatansu, wanda ya faro da yaki da hijabi da alakanta shi da ta'addanci. Bayan rashin nasara, sun yi yaki da dabi'un iyali na Musulunci, Inda suka yi garkuwa da 'ya'yan musulmi suka kwace su daga hannun mahaifinsu, suka ba da su ga wadanda basu yarda da Allah ba. Lokacin da yanayin ayyukansu ya bayyana ga duniya, sun ba da uzuri na 'yancin faɗar albarkacin baki kuma suna fakewa da 'yancin ɗan adam. Sannan suka tada hankulan musulmi ta hanyar kona Al-Qur'ani mai girma da cin mutuncin Littafi Mai Tsarki wanda Al-Qur'ani littafi ne mai hada zukatan musulmi.


Sheikh Musa Al-Khalaf ya jaddada yin watsi da na rashin yin martanin makiya masu tozarta Al-Qur'ani ga kiraye-kirayen kasashen musulmi, inda kasashen musulmi da musuluncu suka nemi dena ci gaba ds aikata wannan cin mutuncin, amma makiya sun yarda da wannan aiki a karkashin inuwar dokar kasa, saboda sun yarda da hakan. sun san rarrabuwar kan musulmi.. Sun san cewa wasu kasashen musulmi ba sa daukar matakai na zahiri kuma suna wadatuwa ne kawai da yin Allah wadai. Da sun san cewa musulmi ba sa zaune tare da kame hannu, da ba su kuskura su ci mutuncin Musulunci da huruminsa ba. Idan da Sweden ta yi hakan ga wani addinin ba musulunci ba da duniya za ta tashi kuma ba za ta zauna shiru ba, mun ga cewa yadda jakadan Isra'ila ya hana kona Attaura.


Yayin da yake ishara da wata ayar kalmar Allah da ke cewa:

 «وانا نحن نزلنا الذكرى وانا له لحافظون” 

ya ci gaba da cewa: Hakika a fadi Allah Ta'ala Alkur’ani mai girma, Allah shi ne majibincin littafin mai tsarki “Hakika mu muka saukar da Alkur'ani Kuma mu muke Kare shi.