Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

11 Agusta 2023

16:47:53
1386345

Jarumtaka A Zantukan Imam Husaini As A Lokacin Yakin Karbala

Cikin darussan Yukurin Ashura Na Imam Husaini As A Watan Muharram akwai Darasin Jarumtaka, wanda idan ya zamanto muka siffantu da wannan siffa din madaukakiya muka rayata zamu kasance cikin wadanda Allah Ta'ala ya ke so da yaba masu.

Jarumta wani karfi ne da ba'a gani da ke cikin zuciya wacce ta ke haifar da dakewar mutum, wacce ita ta ke zamowa karfin mutum, yayin da ya fuskanci abokan gaba da makiya, kuma take karashi jin tsoro wajen fadin gaskiya.

Ya zamo baya jin tsoro gwagwarmaya tare da makiya, ya zamo baya jin tsoron mutuwa.

Imam Husaini As Yana cewa da Hur bin Ziyad bayan ya tare masa hanyarsa zuwa Kufa: Lamarina, Matsayina ba irin matsayin wanda yake jin tsoron mutuwa ba ne, babu abun da yafi mutuwa sauki wajen samun daukakar kai da raya gaskiya, mutuwa a tafarkin samun daukaka ba komai ba ce face sai dai rayuwa madawwamiya, kuma ba komai ba ce rayuwa cikin kaskanci face mutuwa wacce babu rayuwa a tare da ita, shin da mutuwa ne kake bani tsoro!?... Shin zaku iya aikata wani abu sama da kasheni? Maraba da mutuwa akan tafarkin Allah, Amma ku sani ba zaku iya rushe daukakata da share fifikona da girmana ba.


"قالَ الْحُسَيْنُ عليه السلام: لَيْسَ شَأْنى شَأنُ مَنْ يَخافُ الْمَوْتَ، ما أَهْوَنَ الْمَوْتِ عَلى سَبيلِ نَيْلِ الْعِزِّ وَاِحْياءِ الْحَقِّ، لَيْسَ الْمَوْتُ في سَبيلِ الْعِزِّ اِلاّ حَياةً خالِدَةً وَلَيْسَتِ الْحَياةُ مَعَ الذُّلِّ اِلاَّالْمَوْتَ الَّذى لاحَياةَ مَعَهُ، اَفَبِالْمَوْتِ تُخَوِّفُنى... وَهَلْ تَقْدِرُونَ عَلى أَكْثَرِ مِنْ قَتْلى؟! مَرْحَباً بِالْقَتْلِ فيسَبيلِ اللّه ِ، وَلكِنَّكُمْ لاتَقْدِروُنَ عَلى هَدْمِ   .مَجْدى وَمَحْوِ عِزّى وَشَرَفي


Ma'ana Matsayina ya wuce na wanda yake jin tsoron mutuwa wajen fadin gaskiya, ko wajen umarni da kyakkayawa da hani da mummuna,

Matsayi ne na mutumtaka wanda yake sanya mutum rashin jin tsoron mutuwa, kuma matsayi ne da ke sanya mutum yaji baya jin tsoron Azzalumai mahukunta, wanda suke zalumtar Al'ummar da sanya tsoro a zukatansu.

Yazo acikin Surar Al-Imran in da Allah Ta'ala ya ke tabbatarwa da mutane yanayin Jarumatakar Mu'uminai yayinda ake ba su tsoro da Azzalumai da cewa: 

"الَّذِينَ قالَ لَهُمُ النَّاسُ إِنَّ النَّاسَ قَدْ جَمَعُوا لَكُمْ فَاخْشَوْهُمْ فَزادَهُمْ إِيماناً وَ قالُوا حَسْبُنَا اللَّهُ وَ نِعْمَ الْوَكِيلُ"

 " Wadannan da mutane suka ce da su -domin su tsorata su- tabbas akwai mutane da suka yo maku taran dangi don suga bayanku, don haka kuji tsoronsu -kuji tsoron haduwa da su wajen yaki- amma hakan bai sa Mu'uminai jin tsoro ba sai ma ya kara masu imani da dakewa suna masu cewa Allah ya ishe mana kuma madallah da mai kulawa.

Duk da fa an gayawa masu cewa gasu nan fa sun durfafoku da dukkan karfinsu da suka mallaka, kuji tsoronsu fah! amma hakan baisa sun ji tsoron makiya ba, kai sai ma imaninsu da Allah ya karu, karfinsu ya karo da jarumatarsu.

Su ka ce mu munada Allah Ta'ala to akan me zamu ji tsoron wani kuma!? 

Idan muka matsa gaba cikin ayar dake biye da ita Allah Ta'ala yayi nuni da abunda ke haifar da wannan tsoron ga mutane wadanda ba Jarumai ba ne da suke jin tsoro, inda yake cewa:

" إِنَّما ذلِكُمُ الشَّيْطانُ يُخَوِّفُ أَوْلِياءَهُ فَلا تَخافُوهُمْ وَ خافُونِ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ"

Dalinlinsu na jin tsoro ba komai bane face Shaidan da ke tsorotar da wadanda suke yi masa biyayya, iya su kadai yake iya tsoratarwa da sanya masu tsoron azzalumai.

Kaga kenan idan kaga kana jin tsoron fadin gaskiya ko tsoron yin umarni da Kyakkyawa da hani da mummuna ton kasan cewa Shaidan ne ya salladu akanka. Kuma shike nuna ka zabi shaidan wajen yin biyayya sama da Allah Ta'ala.

Dukkan mutanen da suka karbi shaidan a matsayin abun bauta suke masa biyayya to yakan karbe Jarumtakarsu daga wajensu ne ya sanya masu tsoro wannan shine abunda yake faruwa kuma shi ya faru lokacin da Imam Husain As Ya fito amma ba wanda ya goya masa baya sai ƴan kaɗan daga cikin mu'umainai duka akwai su dayawa daga cikin sahabbai da tabi'ai.

Imam Husain As a lokacin da yayi yunkurin Karbala ba wanda ya karba ya dafa masa daga cikinsu, shin babu Mu'uminai ne maau tsarkin zuciya!? da suke kan turbar addini wadanda suke magana da bakunansu wajen kafe addinin Allah shin basu nan! Amsa eh suna nan mana suna ma dayawa manyan sahabban Annabi Sawa kamar irinsu Abdullah bin Abbas Abdullahi bin Umar Abdullahi bin Zubair kuma sun kasance masu kare musulunci da karfin harsunansu kuma sunayin ibadoji yadda ya dace akan lokaci, amma ina! Ina! basu goyawa Imam Husaini As baya ba me sanya suka barsa shi kadai saboda me? 

Saboda sun ji tsoro ne! Tsoron me suke ji suna jin tsoron Yazid ne Azzalumi mai kekasassar zuciya, kuma sunyi abunda yafi jin tsoronsu muni inda suka tsaya gaban Imam Husaini As suna masu hanawa karya fito da maganganunsu na tsoro, suna masu cewa bai kamata ka fita ba.

Su sunji tsoro babu Jarumtaka a tare da su, Imam Husaini Aa yayi Yunkuri ne saboda ya dawowa da Al'ummar Musulmai ruhin Jarumtarkarsu, kuma duk da sunji tsoron mun ga wasu daga cikinsu da suka ji tsoro suka ki taimakawa dan aiken Imam Husaini As wato Muslim bin Aqel bayan Waki'ar Ashura ta faru sun tuba sun dawo sun dake da nuna jarumataka har sai da aka kashesu gaba dayansu,

 Wanda su an yaudare su tare da basu tsoro ta hanyar yada jita jita da Farfagandar cewa Yazid tsinuwar Allah ta tabbata agareshi ya turo da runduna daga birnin Sham zuwa birnin Kufa hakan ya sanya bayan sun dafa ma Muslim daga baya suka janye suka barshi shi kadai, wanda hakan ya sanya yayi shahada a Kufa alhali yana bakonsu, sun fito ba tare da jumawa ba sunyi nadamar abunda suka yi wanda ruhin Jarumataka da rashin tsoro ya shiga jikinsu sun fito fagen daga an kashe su gaba daya. Za mu ci gaba... Insha Allahu