Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

6 Agusta 2023

18:09:54
1385192

SHEKH IBRAHIM ZAKZAKY: TSAKANINMU DA NIJAR YA FI KARFIN DANJUMA DA DANJUMMAI, HASAN DA HUSAINI NE!

Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana takaicinsa a kan yadda makiya ke neman hada rigima tsakanin Nijeriya da Nijar don cimma muradin kashin kansu.

- Inji Jagora Shaikh Zakzaky

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Da yake ganawa da kungiyar Mahaddatan Alkur’ani daga Cibiyar Karatun Alkur’ani mai girma (CQR) a gidansa da ke Abuja, ranar Asabar 18 ga watan Almuharram 1445 (5/8/2023), Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana takaicinsa a kan yadda makiya ke neman hada rigima tsakanin Nijeriya da Nijar don cimma muradin kashin kansu.

Shaikh Zakzaky ya ce: “Abin Allah ya kiyaye, yanzu ga shi haka kawai, haka siddan, Faransa da Amurka sun zo za su yi amfani da Nijeriya su kai wa Nijar hari. To, wannan abu da ban-al’ajabi shi ma. Don mu tsakaninmu da Nijar muna ganin abu daya ne, in ma Kudu suna ganin ba su a ciki, to mu nan Arewacin Nijeriya an yi daular Shehu Usman Danfodiyo, da kuma Daular Borno. Wadannan daulolin guda biyu, su aka tsaga su tsakanin Nijer da Nijeriya.”

Ya ce: “Kun ga da nake ce muku Gazargamu shi ne babban birnin Borno ko? To har yanzu ganuwar garin na nan, don an bar garin da wadansu gine-gine. To kun san rabin ganuwar garin yana Nijar ne (yanzu haka), rabin ganuwar yana Nijeria, an tsaga biyu ne kan iyaka din. Lokacin da ake tsaga kan iyakan nan, ba su yi la’akari da tarihinmu ba.”

Jagora ya cigaba da cewa: “Kamar yadda nake ce muku, Borno an raba ta hudu, Nijeriya, Kamaru, Chadi, da Nijer, duk Borno ne. Sannan kuma idan ka bi Daular Shehu Usmanu, tun daga Borno din har ka kai Sakkwato kowane gari an raba shi biyu ne. Ainihin za ka ga Hadejia akwai wani bangare ya koma Nijar (a yanzu bayan da Turawa suka tsaga), Gumel wani bangare ya koma Nijar, in ka je kana wuce Maigatari, idan ka tsallaka Gumel kake, amma ya koma Nijar. Kazaure ma haka nan wani wuri yana Nijar. 

“To Daura ma haka, mafi yawan Daura ma Nijar ta koma. Mafi yawan Daura tana Nijar ne (a yanzu). Katsina ma an raba ta biyu, da Katsinan Maradi da Katsinan Katsina. Haka aka raba. Sannan kuma Daular Gobir ta da, an raba ta ne, wasu na bangaren Nijar, wasu na Nijeriya. Mahaifan Shehu Usman Danfodiyo, Marata, tana cikin Nijar.”

Shaikh Zakzaky yace: “Saboda haka mu tsakaninmu nan da Nijar, ya wuce kace tsakanin Danjuma da Danjummai, don Danjuma da Danjummai suna suka tara, mu Hasan da Husaini ne, uwarmu daya ubanmu daya. An fahimta ai!”

Yace: “Su ne Hasan, tunda mahaifan babanmu Shehu Usman Danfodiyo yana wajensu, sabida haka su ne Hasan, mu ne Husaini din. Mu bamu san yadda za a yi a ce ko da mafarki wai muna fada da junanmu ba. Amma ka ga wadannan la’anannun mutane, sun zo wai su ne za su yi amfani da nan su je su kai ma ‘yan uwanmu hari. Mu kashe kanmu kenan ko?”

Ya nesanta al’ummar Nijeriya daga al’amarin da cewa: “Na ji wadansu ‘yan Nijar suna cewa Nijeriya za su kawo musu hari. Nace, a’a ku daina cewa haka nan, in ma abin ace an kai muku hari ne, -Allah Ya sauwake. Ina fata ba zai auku ba. To ba mu ne muka kai muku hari ba, ainihin an yi amfani da wani ne, wanda aka ce shi ne shugaban kasa, aka je aka kai muku hari. Ba dai Nijeriya ba, ba da yawunmu ba, ba da saninmu ba, ba da amincewarmu ba, ba yadda za a yi mu kashe kanmu! Saboda haka, ba Nijeriya za ta kai hari ba, wasu ne za su yi amfani da Nijeriya. Kuma sun sha yi.”

Shaikh Zakzaky, ya ba da misalan yadda Amurka ta rika hada fada tsakanin kasashen da suke makwafta ko tare da juna, kamar yadda ta hada yakin da aka shekara takwas ana yi tsakanin Saddam Husaini daga Iraq da kasar Iran, alhali tuntuni kasashen Iran da Iraq suna daukar kansu a matsayin al’umma guda ne.

Ya kuma ba da misalin yadda Amurka ta hada fada tsakanin Saudi Arabiyya da Yemen. Da kuma yadda Faransa da Amurka suka hadu wajen haddasa fadan Kabilanci tsakanin kabilun Hutu da Tutsi a Afirka ta Yamma inda suka rika kashe junansu, da makamantansu.

Sannan ya yi gargadi da cewa: “Don mu gargadi masu zumudin za su je su kaima Nijar hari, su sani cewa za su yi babban kuskure. Ba mu fatan ya auku, amma in abin su yi ne, za su yi ma makiya aiki ne, kuma in ba su burge makiyan ba karshe, yadda aka rataye Saddam shi ma wannan Agwalagwa din haka za su rataye shi. Basu ga amfaninshi ba (a lokacin), ya gama amfani.”

Jagora yace: “Tunkuda shi za su yi ya yi barna, shi ya dauka zai zama gwarzo ne. Yanzu an ce har ya katse Lantarki, ya kuma rufe Boda (kan iyaka). To ai duk wannan bashi da iko ma ya yi bisa ka’ida. Ba an ce za a yi Damukuradiyya ba ne? Wai zai kai Damukuradiyya ne Nijar ba? To Damukurdiyya ne ya bashi damar ya katse wutan lantarki? Wutan landarkin nan wa ya katse ma? Sojojon da suke mulki ya katse ma ko mutanen Nijar? Mutane ne suke amfani da shi. Kuma ciniki ne aka yi ai, yarjejeniya ne aka yi ai, suna biya ne, ba kyauta ake basu wutan ba.”

Yace: “Kuma ECOWAS, ba kungiya ce ta tsaro ta soja ba, “Ecowas” kamar sunan shi ne ‘Economic Community’, ainihin sha’anin Tattalin arziki ne ya hada su, ba yaki ba. Ba inda aka rubuta a cikin tsarinsu za su kai yaki. Ba aikinsu ba ne. Amma yanzu aka zo wai da sunan Ecowas ne (za a kai hari). To kuma yanzu sun fara tunanin Nijeriya ne ma da Nijar za a kai hari. Allah Ya sauwake.” 

A karshen ganawarsa da Gwanaye da Alarammomin, Shaikh Zakzaky ya jaddada musu cewa, ba mu da makamin da ya wuce riko da Allah Ta’ala. Mu koma ga Allah Ta’ala.

Ya kuma yi addu’a da fatan neman taimakon Allah Ta’ala, tare da kira ga re su da cewa: “A cigaba da Ihtimami da Alkur’ani kamar yadda ake yi, Alhamdulillahi mun godewa Allah. Wannan ni’ima ce babba. Mun godewa Allah da wannan ni’ima. Ba wata ni’ima kamarta, wanda duk Allah Ya bashi Alkur’ani, to kar ya ga an ba wani wani abu ya ga ya fi shi, domin shi yana da abin da ya fi komai.”

@SZakzakyOffice

06/08/2023