Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

1 Agusta 2023

13:55:51
1384225

Iran Na Son Kwanciyar Hankali Da Zaman Lafiya A Nijar

Iran na son samun kwanciyar hankali da zaman lafiya da walwala a Jamhuriyyar Nijar Afirka

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Bayan abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya sanar da cewa, Iran na son samun kwanciyar hankali da zaman lafiya da walwala a wannan kasa ta Afirka, tare da fatan ci gaban da ake samu zai kai ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma samar da ra'ayoyin al'ummar Nijar.