Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) - ABNA ya habarta cewa, masoya Imam Hussaini (a.s) sun gudanar da tattaki a birnin Michigan na kasar Amurka, domin tunawa da shahadarsa, tare da yin Allah wadai da cin mutuncin alfarmar kur’ani mai tsarki.
A cikin wannan taro masu muzaharar suna tafiya me tare da wani jirgi mai saukar ungulu dauke tutar Imam Husaini (AS).