Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

30 Yuli 2023

16:52:12
1383623

An Gudanar Da Muzaharar Ashura Ta Shekarar 2023/1445 A Birnin Kano Najeriya

A ranar Jumma'a 28/07/23 daidai Hijra 10/01/1445, 'yan uwa Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky na Da'irar Kano da kewaye suka gabatar da gagarumar Muzaharar Ashura.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, An faro Muzaharar ne daga Shatale-talen Tal'udu cikin birnin Kano aka miko Titin Gwauron Dutse aka shie Gwauron Dutse har zuwa Gidan Isyaka Rabi'u aka shigo ta Gwammaja daura da gidan Mumbayya aka kammala a filin Dalar Gyada.

Muzahahar ta samu halarta duban daruruwan 'yan uwa Maza da Mata Yara da manya cikin shigar bakaken kaya da ke alamta alhini da bakin cikin abin d ya faru a wannan Ranar ta Ashura.

Mahalart Muzaharar suna rike da Tutoci masu launika daban daban da suke dauke rubuce-rubuce da suke bayyana zaluncin Banu Umayya akan Zuriyyar Annabi (Sawa) Yan uwa sun yi shiga tawaga-tawaga. Akwai Harisawa rukuni-rukuni Maza da Mata daban daban, da tawagar Matasa kashi kashi cikin shiga mai ban sha'awa da kuma tawagar Yan Chaji-Chaji da Zainabawa da Intizar da tawagar yan JASAS, akwai Fulani da Makarantun Fudiyya daban daban da sauran yan uwa Maza da Mata.

Muzaharar ta cika sosai gaske, an yawan da har aka yi jawabin rufewa wasu ba su iya shigowa Unguwar Gwammaja balle su karasa zuwa Filin Dalar Gyadi, abin da ya hada mai rubuta Rahotan nan kenan don haka bai iya riskar jawabin Karshe ko samun hotunan dandazon yan uwan da suke cika filin makil ba. Mutane masu kallo suna mamakin yawan yan uwan da suke gani a Muzaharar ta Ashurar bana, har an ji wani yana cewa 'Wallahi Mutanen nan kullum kara yawa suke fah'.

An kammala lafiya

Internet Forum