Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

30 Yuli 2023

10:59:00
1383468

Taron Tuwairij Mafi Girman Taron Ta'aziyyar Imam Husaini As A Duniya

An Gudanar Da Taron Tattakin Tuwairej Inada Mahalarta Taron Suke Ta Maimaita Kalmar {Labbaika Ya Husain} A Tsakanin Hubbare Guda Biyu

A ranar Asabar 29 ga watan Yuli 2023 daidai da (10 ga Muharram shekara ta 1445 bayan hijira) dimbin muminai sun gudanar da bukukuwan tunawa da Ashura da shahadar Imam Husaini (a.s), yayin da dubban daruruwansu suka zo birnin Karbala domin tunawa da wannan lokaci.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, an kaddamar da taron "Tattakin Tuwairej" a birnin na Karbala tare da halartar dimbin jama'a, a yayin da suka yi tattaki zuwa hubbaren Imam Husaini. tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, inda daga hubbarensa sukai tattakin zuwa haramin dan uwansa Abul Fadl Abbas “amincin Allah ya tabbata a gare shi”, cikin ayyukan ibada da ake yi bayan an yi sallar azahar a ranar goma ga watan Muharram.

Gudun Tuwairej dai na wakiltar daya daga cikin manya-manyan tarukan dan Adam da ke gudana a fadin duniya kuma ana gudanar da shi ne a duk shekara da tsakar rana a ranar goma ga watan Muharram domin tunawa da shahadar Imam Husaini, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Miliyoyin maziyartan Iraqi da Iran da Larabawa da na kasashen waje ne ke halartar sa, kuma ana fara shine daga yankin Qantara Al-Salam da ke Karbala zuwa ga hubbaren Imam Husaini, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a tsakiyar tsohon birnin, da tsawonsa ya kai km 2, inda mahalarta suke karuwa kowace shekara.

Mahalarta taron Tuwairej sun yi ta rera taken "Muna kan hidimar ka ya Husaini" a matsayin martani ga kiran Imam Husaini (a.s) na ranar Ashura na cewa, "Ko akwai wani mai goyon bayan da zai taimake mu?"

Yadda Aka Kafa Wannan Taron

Wadannan taruka kamar sauran ayyukan ibadoji na raya lamarin Husaini, sun shiga matakai na takurawa da haramci har sai da a kai ga yinsu a boye don tsoron kada mahukuntan kasar su bi sawun su da suka sanya dokar hana gudanar da wadannan taruka a zamaninsu.

Kuma masanin tarihi Karbala’i Saeed Rashid Zamizam yana cewa: “Ranar da aka kafa wannan muzaharar ta zaman makoki a daya daga cikin ruwayoyin ita ce shekara ta 1855 miladiyya, a wata ruwayar kuma a shekara ta 1872 miladiyya, ma’ana shekarun wannan muzaharar ta gabaci shekaru 150."

Ya kara da cewa, wanda ya assasa wannan makoki yana daya daga cikin fitattun mutanen birnin Karbala da ke gundumar Hindi (Tuwairej), wanda ake kira Mirza Saleh Al-Qazwini, inda ya kasance yana gudanar da taron ta'aziyya a cikin kwanaki goma na farko na watan Muharram a gidansa, sannan sai ya hau dokinsa tare da gungun masoya Ahlul-baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, sai su fara gudu suna rera taken goyon bayan Husaini, inda ya zamo da zarar mutanen Karbala sun gansu sai suna ta gudu suna shiga cikin ayarin makokinsa.

Zamizam ya yi nuni da cewa, a lokacin da Mirza Salih al-Qazwini tare da masu makokinsa suka isa yankin Bab Tuwairij, Qanɗaratul Salam, sai suka yi sallar azahar, bayan haka kuma suka sake tashi domin gudanar da makokin sassarfa na Tuwairij suna masu tasowa daga titin Tawiraj zuwa kasuwar Ibn Al-Hamza daya daga cikin kasuwannin tsohon birnin Karbala, inda ta bi ta kasuwar Al-Saffarin da Alawi, sannan ta wuce kasuwar Khafafin, sannan su nufi haramin Imam Husaini (a.s) sai wuce su tafi wurin dan uwansa Abal Fadl Al-Abbas, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Kuma ya ci gaba da cewa: “Bayan sun shiga hurumin Mawla Abal Fadl Abbas, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai muzaharar ta nufi wurin sansanin Husaini mai girma, a nan ne mutanen Karbala suke shirya wata tanti domin su kona ta domin tunawa da abin da sojojin Yazidu suka yi na kona tantin Imam Husaini, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da alayensa da sahabbansa a ranar Ashura”.

Gargadin Da Gwamnatin Ba'as Ta Yi Akan Hana Gudanar Da Shi

An ci gaba da gudanar da wadannan taruka har zuwa shekara ta 1990 miladiyya, amma bayan boren Sha’aban a shekarar 1991, gwamnatin Baath ta kafa dokar hana gudanar da su gaba daya, amma jama’a sun dage da gudanar da su, lamarin da ya sa jami’an tsaron Saddam suka kaddamar da kame-kame da kisa ga mahalarta taron.

Jabir Talqani daya daga cikin ayarin tawagar jaruman Karbala ya bayyana cewa: “Mahukuntan gwamnatin Ba’ath sun kasance suna baza dakarunsu a kan titin wucewar wannan makoki a ranar goma ga watan Al-Muharram, domin sanya ido kan masu gudanar da wannan aikin makokin, musamman matasa,sai suna sanya masu jan fanti a jikinsu domin su bambance su tare da kama su”.

Al-Talqani ya kara da cewa suna bibiyar wasu daga cikin matasan da suka halarci taron suna kai su zuwa motocin daukar marasa lafiya suna ta ihun cewa wai “Ba shi da lafiya ne” amma gaskiyar magana ita ce sun kama wadannan matasan ne.

Al-Talqani ya kara da cewa, “ Amma ba a iya sauke tutar Imam Husaini, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba, duk da irin wahalhalun da kasar nan ta shiga, kuma duk da mamayar shugabannin mugaye da kuma hana ayyukan Imam Husaini, saboda Allah ya ki dusashe haskensu."

Bayan shekara ta 2003, ayyukan Imam Husaini su sake dawowa, a bayyane da tsari, kuma ana ci gaba da samun karuwa daga ciki da wajen kasar Iraki, kuma ana daukar sa a matsayin daya daga cikin fitattun ayyukan Ibada na Husainiya a ranar goma ga watan Muharram, inda dimbin jama'a ke halartarsa.

.................