Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

29 Yuli 2023

07:04:55
1383046

An Gudanar Da Muzahar Ashura Ta Shekarata 1445H Manyan Biranen Najeriya

Ranar Juma’a 10 ga watan Almuharram 1445 (28/7/2023), fiye da birane da kauyuka 50 ne a fadin Nijeriya ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) suka gudanar da Muzaharorin Ashura, don juyayin ranar Shahadar Imam Husaini Bin Ali Bin Abidalib (AS) wanda rundunar makiya Allah bisa umurnin Yazidu dan Mu’awiyya suka kashe shi a Karbala, a shekara ta 61 bayan Hijira.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - kamar yadda rahoton ya bayar Dukkanin garuruwan an gudanar da Muzaharorin lafiya, in banda Abuja, inda jami’an tsaro suka bude ma masu Muzaharar wuta, sai dai bisa kiyayewar Allah, izuwa yanzu ba a samu Shahidi ba.

CIBIYAR WALLAFA tare da taimakon Wakilai, ta iya tattaro hotunan wasu daga garuruwan da aka gudanar da Muzaharorin, kamar yadda kuke gani.

http://www.cibiyarwallafa.org/hotunan-muzaharorin-ashura-1445-a-nigeria/