Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

28 Yuli 2023

13:53:01
1382885

Mutanen Yaman sun fito kan tituna domin gudanar da Muzahara Ashura

Al'ummar kasar Yemen sun ci gaba da raya ayyukan Ashura ta hanyar gudanar da manya-manyan taruka da jerin gwano a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A yau ne ‘yan kasar Yemen suka fito kan tituna inda suka gudanar da tarukan juyayin Ashura a garuruwa irinsu Sana’a, Ab, Al-bayda, Marib da Sa’ada.

Al'ummar kasar Yemen sun jaddada ta hanyar gudanar da tattaki na tunawa da ranar Ashurar Husaini As , inda suka ce: tunawa da wannan wakiah na nuni da soyayya da kaunarmu ga Imam Husaini, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma nuna matsayinmu na addini da na dabi'a a kan mahara da masu aikata laifuka.

A cikin bayanin mahalarta taron sun bayyana cewa: Muna riko da matsayinmu na al'amuran al'ummar musulmi, kuma a samansu duka shi ne lamarin Palastinu.