Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

23 Yuli 2023

18:02:58
1381727

“Wannan al'amari na rayar da gidan Manzon Allah (S) kamar yadda Imam Sadiq (AS) ya ke cewa “Allah ka yi gafara ka yafe wa wanda ya raya al'amarinmu”.

__Shaikh Yakub Yahya Katsina.

“Wannan al'amari na rayar da gidan Manzon Allah (S) kamar yadda Imam Sadiq (AS) ya ke cewa “Allah ka yi gafara ka yafe wa wanda ya raya al'amarinmu”.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ci gaba da kawo maku bayanan Ashura da ke gudana a dukkan sansan Duniya gaba daya yama ya kawo maku tsakure na bayan shekh Ya'akub Yahaya Katsina shugaban mabiya mazhabar Iyalan gidan Annabi na yankin Katsina tarayyar Najeriya karshin jagorancin Shekh Ibarahim Ya'akub Alzazaky inda malam ya ci gaba da cewa: "Cikin raya al'amarin hadda wannan majalis ɗin, wannan majalis wanda suke nuna magoya bayan Annabi (S) tsantsa, zun-zurutun su, kasan wannan shi ke bayyana su wanene waɗannan.

To mu akwai wani alami wanda aka banbanta da shi, shi ne baƙaƙen kaya, baƙaƙen kaya na nuna jaje da damuwa, baƙaƙen kaya a kan nuna jaje da damuwa sai ya zama ba ’yan shi'a ne kawai ke yi ba hadda al'ummar musulmi da yawa suna yin wannan, suna sa baƙaƙen kaya domin akwai waɗanda aka riƙe masu albashi sai suka yi yajin aiki duk sai suka sanya baƙaƙen kaya, suna yajin aiki an hana su albshin su, alama ce ta nuna takaici.


Ballantana mu namu bisa koyarwa ne, ranar wafatin Imam Ali (A.S) ance Imam Hassan (A.S) ya fito da baƙaƙen kaya da baƙin rawani, ya zo ya yi huɗuba, ya yi wa mutane jaje, ya yi masu ta'aziyya, da baƙaƙen kaya a jikin shi da kuma rawani.


To akwai kuma wurare daban-daban waɗanda wurare ne na damuwa, inda ake amfani da baƙaƙen kaya, in ma mun sanya ina ruwanka, in mun sa baƙaƙen kaya ina ruwanka, laifi ne asa baƙin kaya? a wace shari'a ɗin, in zunubi ne wa za a ba? kai za a ba da kake kallo kana suka koko mu da muka sa? in laifi ne wa za a ba? "Mu", in kuma lada ake samu wa ya yi asara? "Shi" da bai sa ba, yana suka.

__ Cikin bayanin Shaikh Yakub Yahya Katsina a wajen zaman Ashura rana ta ɗaya.