Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

22 Yuli 2023

22:42:52
1381511

TARON KARAWA JUNA SANI NA TUNAWA DA 25 YULI KARO NA (9) A BIRNIN ABUJA

Yadda taron karawa juna sani ya gudana a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya don tunawa da wakir 25 ga watan Yuli 2014m cikin hotuna.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A yau Asabar 22 July, 2023 harkar Musulunci karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Ya'qoub El-Zakzaky, ta gabatar da Conference akan tunawa da Waki'ar 25th wanda ya gudana a garin Zariya a Shekarar 2014, wanda Sojojin Najeriya suka bude wuta akan masu gudanar da Muzahara Qudus suka kashe mutane 34 ciki harda ƴaƴan Jagora guda 3, Sayyid Ahmad, Hameed da Mahmud.

Taron wanda ya gudana a Ibro Hotel Dake Wuse Zone 5, inda aka gayyato mutane daban daban ciki da waje Kasar nan suka gabatar jawabi a Muhallin taron, bayan kammala jawabin nasu Malama Zeenah Ibrahim ta gabatar da jawabin rufewa, sannan aka baje kolin hotuna na tarihi na nuna Rashin mutunta Dan Adam na abunda ya faru da kuma nuna hotuna na tarihi Shuhada.

22/07/2023

AliAssajjad Ibn Taheer

Auwal Fudiyyah

Naziru Ahmad Addarkawy