Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

22 Yuli 2023

13:38:59
1381293

Jaridar Kad Hizbullah Bugu Na 402 Ta Fito Da Taken "Dauwamar Musulunci Ya Samu Ne Da Albarkar Ashura".

An buga jaridar Khat Hizbullah ta mako-mako fitowa ta 402 mai taken "Dauwamar Musulunci ta samu ne da albarkar Ashura".

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A bisa munasabar zagayowar watan Muharram, jaridar Khad Hizbullah ta yi nazari kan fa'idab da sakamakon Qiyam din Aba Abdullahil Hussein, amincin Allah ya tabbata a gare shi, in da tayi bitar maganganun jagoran juyin juya halin Musulunci.

Jawabin makon wannan jaridar ta kungiyar Hizbullah mai taken " Zamowa Mai Addini Dan Kasa, sune sirrin ci gaba da nasara" ya amsa tambayar cewa mene ne sirrin shirin makiya wajen bata kishin kasa na Iraniyawa?

Mujallar Hizbullah ta wannan makon ta sadaukar da wannan bugun ne ga tsarkakan ruhin shahidun tsaro na Turawa Kamal Kursel.