Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

20 Yuli 2023

15:07:53
1380806

Cikin Jerin Shirye-shiryen Gudanar Da Taruka Na Watan Muharram Shekarata 1445h

Manufofin Futowar Imam Husaini As

Imam Husaini (a.s) fitila ce ta shiriya, yana haskaka hanyar gaskiya da nagarta da adalci, kuma yana shiryarwa zuwa ga mafi daidaiton lamurra, jirgin ceto cike yake da wadanda suka hau shi a cikin guguwar ruwa na zalunci, girman kai, fasadi, rudu, karkacewa daga usulai da Allah ya halicci mutane a kansu.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya ke kawo maku bayanai dangane Ashura yau ma ya kawo maku wani muhimmin tunatarwa dangane da tsayuwar Imam Husaini As da manufofinta.


"اَلسَّلامُ عَلَيْكَ يا أبا عَبْدِاللهِ وَعَلَى الأَرْواحِ الَّتي حَلَّتْ بِفِنائِكَ، عَلَيْكَ مِنّي سَلامُ الله أَبَداً ما بَقيتُ وَبَقِيَ اللَّيْلُ وَالنَّهارُ، وَلا جَعَلَهُ اللهُ آخِرَ الْعَهْدِ مِنّي لِزِيارَتِكُمْ، اَلسَّلامُ عَلَى الْحُسَيْنِ، وَعَلى عَلِيِّ بْنِ الْحُسَيْنِ، وَعَلى أَوْلادِ الْحُسَيْنِ، وَعَلى أَصْحابِ الْحُسَيْنِ. 


Imam Hussain (a.s), fitilar shiriya ne, yana haskaka hanyar gaskiya, da kyautatawa, da adalci, kuma yana shiryarwa zuwa ga mafi daidaito hanya kuma jirgin ceto ne da ke cike da wadanda suka hau shi domin tsira daga guguwar ruwa na zalunci, da girman kai, da fasadi, da bata, da karkacewa daga abubuwan da Allah ya halicci mutane akansu.


Shekara dubu da dari uku da tamanin da hudu, Imam Husaini (a.s) fitila ce mai haskakawa, tana haskaka duniya, tana watsuwa a sassanta guda hudu, gabas, yamma, arewa da kudu, kuma tana aika haskenta zuwa ga zukata da suka gaji suka takura, yana rayar da su, yana sabunta musu gabobin imani, da dasa shauki a cikin ruhinsu, sanin kansu da abunda ya hau kansu.


Imam Hussain (a.s) shine wanda yake rayar da rayuka, yana rayar da dabi’u, da rayar da ruhin dan Adam, da raya addinin annabawa da manzanni Allah.


Imam Al-Hussain (a.s), shi daya ne daga cikin ayoyin Allah, mai shiryarwa zuwa ga Allah, bisa tafarkin Allah, majiɓincin Allah, majiɓincinsa, mai shaida a kan addinin Manzon Allah.


Shi ne Al-Hussain (a.s) shugaba kuma abin koyi, zamani ba ya kama shi, zalunci ba ya kewaye shi, kuma azzalumi ba ya hana shi tasirinsa.


Shi ne Al-Hussain (a.s) da zukatan salihai, na kwarai da masu ‘yanci suka taru a gareshi, suna ketare shingen addinai da mazhabobi da ra’ayoyi domin su kai gareshi kowanne daga cikinsu yana samun sha’awar haduwa da shi da bukatarsa. 


Al-Hussain (a.s) bai kebanta ga wasu masu addini su kadai ba ko mazhaba kowa na shi ne, ba ya da iyakar kasa, ko takaitashi da wani yare ko kabila ko launin fata.


Kuma Al-Hussain (A.S) shine mai rike da tutar gaskiya tun da aka samu fuskanci tsakanin gaskiya da bata a farkon al’umma ta farko, tun da hassadan Shaidan ga Adam wanda Shaidan ya ki amincewa da kyawawan dabi’unsa, tunda ya yi rantsuwar batar da ‘ya’yan Adam.


Al-Hussein (a.s) shi ne magajin dukkan wadanda Allah ya zaba domin ya ceci bil’adama da shiryar da su zuwa ga gaskiya da nagarta da adalci. Duk wanda yake da mutuntawa da mutunci yana da misali abin koyi ga Husaini (a.s), wanda ya kasance mai neman gyara yana da misali ga Husaini (a.s), kuma duk wanda ya nemi gaskiya yana da misali mafi girma ga Husaini (a.s), wanda kuma yake son ya fuskanci zalunci da girman kai to Kyakkyawaan misalinsa shi ne Imamul Husaini (a.s) shi ne mafificin abin koyi gareshi.


Ya ku dukkan al’ummar duniya, ku zo ga Husaini (a.s), ba bukatar kawai kuyi ta kuka da makokinsa ba kawai a a ana bukatar ku ku zo gare shi, ku karanta waye shi, ku fahimce shi, shi naku ne gaba dayanku kamar yadda manzan Allah ya kasance gare ku baki daya.


Ku zo ya ku Musulmi da Shi’a da Ahlus-Sunnah zuwa ga Hussaini (AS), da abin da kuke buqatar ku canza ko ku samu gaskiyar hakika daga rigingimun da kuke cikinsu Imam Husain ya ba ku mafita, ku zo ya ku Kiristoci, ga Hussaini, domin a gareshi akwai abun ke ga Al-Masihu Isa dan Maryama, ya ku Yahudun duniya ku zo ga Al-Husaini (AS) domin a wajensa akwai abun da ya kasance a gurin Annabi Musa da Harun As Ku zo ya ku ‘yantattun duniya, ba za ku sami ‘yanci na gaskiya ba sai a wajen Husaini, kuma al-Hussain ya bude muku kofofinsa.


Marubuci kuma mai binciken kur’ani dan kasar Lebanon ne ya rubuta, Mista Bilal Wahbi

......