Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

19 Yuli 2023

11:29:52
1380490

An Gudanar Da Taron Canza Tutar Ƙubbobin Haramin Karbala

A daidai lokacin shigowar watan Muharram a daren ranar Talata daren daya ga watan ne aka gudanar da bikin canza tutar hubbaren Imam Husaini (AS) da Abul Fadlul Abbas (AS) a daren farko na watan Muharram a gaban dubban maziyarta.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, An gudanar da wannan Taro ne a farfajiyar Husaini Sharif, tare da halartar malaman addini da dimbin muminai.

Wadanda suka halarci wannan taro sun bayyana tofin Allah tsine da adawa da cin mutuncin kur'ani mai tsarki tare da rera taken "Taj Taj Ali ala Ras al-Sayyid al-Sistani".