Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

17 Yuli 2023

12:06:45
1379965

Cikin Jerin Shirye-shiryen Gudanar Da Taruka Na Watan Muharram Shekarata 1445h Tehran

'Yan Sandan Kula Da Zirga-zirgar Ababen Hawa Na Tehran Sun Fara Shiri Don Kulawa Gudanar Da Taruka Na Watan Muharram 1445h

Shirye-shiryen Jami'an 'Yan Sandan Kula Da Zirga-zirgar Ababen Hawa Na Tehran Don Kulawa Gudanar Da Taruka Na Watan Muharram 1445h

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Mataimakin daraktan kula da harkokin zirga-zirga da al'adu na rundunar 'yan sandan Tehran ya bayyana cewa: A gobe Talata ne za a fara gudanar da taruka na watan Muharram kuma rundunar 'yan sandan babban birnin kasar tayi nazarin tsare-tsare na musamman na zirga-zirgar ababen hawa a wadannan kwanaki.

Kanar Ehsan Momeni ya ci gaba da cewa: Baya ga wuraren da ake kafa tarukan zaman makoki na ranakun Al-Muharram, an kuma samar da wuraren da ake gudanar da addu'o'i domin tarbar 'yan kasa da makokin Husseini, sannan masu gudanar da muzaharar tattaki su zabi wuraren da suka dace domin kafa runfunansu don kada ya haifar da cinkoson zirga-zirga.


Ya kara da cewa: Dole ne wadannan runfuna su kasance da tazarar da ta dace daga magudanar ruwa da kuma murabba'ai na mahadar hanyoyi sannan kuma su kasance da tazarar kusan mita 150 daga wadannan hanyoyin.