Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

13 Yuli 2023

10:03:03
1379166

Ranar Mubahlah; Tabbatacciyar Hujjah Bisa Ingancin Musulunci Da Alfaharin Mazhabar Ahlul Baiti (AS).

Girman Mubahlah ya sanya ta a matsayin daya daga cikin mafi wanzuwar al'amura a tarihin Musulunci, amma ba a yi nutso wajen bayanin hakika da matsayi dake tattare d aita ba kamar yadda ya kamata.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) - ABNA ya kawo maku takaitaccen bayani kan batun Mubahal, wanda yake lamarin Mubahala na daya daga cikin manya-manyan al'amura a tarihin Musulunci, kuma wata hujja ce mai karfi da ke tabbatar da halaccin Shi'a da kuma darajar Ahlulbaiti As.


Haka Allah ya nufa a ranar Mubahala ya sanya tsineneya tare da wadanda ba su yarda da gaskiya ba, domin ta bayyana hakikanin gaskiyar addinin Annabi Khatam Sawa.


Muhimmin waki'ar Mubahalah ya faru ne gabanin babbar waki'ar Ghadir a shekara ta tara bayan hijira. Bayan kafa harsashin ginin sabuwar gwamnatinsa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallama ya rubuta wasiku zuwa ga shugabannin gwamnatoci tare da kiransu da su amsa kiransa. Ya rubuta wasika zuwa ga Bishop na Najran kuma ya nemi Kiristocin Najran da su karbi addinin gaskiya. Domin suna daukar kansu a matsayin masu gaskiya, sai suka ki karbar kiran da Annabi ya yi masu, amma sai suka yanke shawarar tura wasu manyansu wurin Annabi su tattauna da shi a kan ingancin da'awarsa. Tawagar Najranawa goma sun tattauna da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam) a masallacin Madina, amma da dukkan bangarorin biyu suka dage a kan haqqin su, sai aka daidaita, aka yanke shawarar cewa za su hadu a wani wuri goben ranar domin yin Mubahalah (wato tsineneniya kan halaka wanda baya kan gaskiya don bayyanar da mai gaskiya da lamarinsa).


A ranar alqawarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallama ya bayyana a cikin haske kamar rana mai haske tare da wata mai haske da taurari masu haskakawa sun halarta a wajen da akai Alkawarin haduwa bayan sun iso sai Annabi ya zauna a durkushe ya shirya kansa domin gudanar da Mubahlah.


Lokacin da idanun kiristocin Najran suka hango fuskõkinsu masu haske tsarkakakku daga nesa, sai suka ce: Su wane ne wadannan da suke tare da Muhammadu? Sai suka ji amsar cewa: Wanda yake gabansa shi ne dan uwansa kuma mijin diyarsa kuma mafi soyuwa a gare shi. Waɗannan yara biyu, ’ya’yansa daga ‘yarsa; Kuma waccan matar ita ce Fatima ‘yarsa, wacce ta fi soyuwa a gare shi.


Da suka ji haka sai suka ce: Wallahi Muhammadu yana zauna kamar yadda annabawa suke zauna suna yin salla. Da Muhammadu ba ya da gaskiya da bai zo da mafi soyuwar mutand ba a gareshi, kuma idan ya yi Mubahalah da mu, kafin shekara ta kare, ba za a samu Kirista ko daya ba a duniya. 


Domin Mun ga fuskokin da idan sun roki Allah zai kawar da tsauni daga inda yake.


Abin da ake bukata na Mubahlah shi ne a kirawo mafi soyuwa kuma mafi cancantar mutane, kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallama ya kirawo 'yan uwansa a matsayin abokan tarayya don halartar wannan taro mai matukar muhimmanci, kuma wannan Mubahlah ta zama hujja mai karfi na halaccin wilayar Ali, amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, da darajar Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su.


Ba ya ga da abubuwa na musamman da waki’ar Mubahlah ta tarihi ta kunsa, bayyananniyar ayar Mubahlah ta bayyana girma da daukakar Amirul Muminin, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma kara fassara sifofinsa da Annabi mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, na daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a wannan rana mai girma. Rantsuwar Mubahalah hujja ce ta Alqur'ani mai girma da ke nuna falalar Ahlul Baiti (a.s) da halifancin Amirul Muminina Ali (a.s).

 

Ayar Mubahalah ta tabbatar da su wane ne bayin Allah na kusa da nagartattu kuma mafi soyuwa.


Kamar yadda Allameh Tabatabai ya fassara ayar Mubahalah, yana nuni da cewa Amirul Muminin, Sayyidah Zahra, da Hasnain (a.s) sun kasance masu tarayya a aikin Manzon Allah wajen kira zuwa ga tauhidi da tabbatar da gaskiyar Annabi da kuma tabbatar da gaskiyar Manzon Allah (saww) da addinin musulunci mai tsarki da kuma watsi da shirka a cikin akidar kiristoci Najran.



Babu shakka, ayar Mubahlah ita ce mafi ingancin hujjar shugabancin Amirul Muminin, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma nadinsa a matsayin magajin annabi sawa, ta yadda Imam Riza, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a cikin Ihtijaj dinsa, ya yi la’akari da ayar Mubahlah da ayara da taffi zama mafi kyawun hujja akan halifancin Amirul Muminina.


Shaidar da ke cikin aya ta 61 a cikin suratu Ali-Imrana ita ce kalmar “kanmu” da ke nuni ga Sayyidina Ali, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

 «فَمَنْ حَاجَّک فِیهِ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءَک مِنَ الْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَ أَبْنَاءَکمْ وَ نِسَاءَنَا وَ نِسَاءَکمْ وَ أَنْفُسَنَا وَ أَنْفُسَکمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَتَ اللَّهِ عَلَى الْکاذِبِینَ؛

Kuma wanda ya yi jayayya da ku game da Annabi Isah As, bayan kun san yanayinsa, ku ce: Ku bari mu da ku mu kira yaranmu da yaranku, matanmu da matanku, da suke a matsayinmu mu da kawukanmu da kawukanku, sa'an nan mu tashi mu tsayu mu sanya la'anar Allah a kan makaryata tsakanin mu da ku.


Imam Riza Alaihis Salam a cikin wata tambaya da Ma'amun ya yi masa, ya dauki aya mafi girma da ta sauka a matsayin Amirul Muminin Sallallahu Alaihi Wasallama ita ce ayar Mubahlah, kuma abin ban sha'awa ne. Imam Riza, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai ambaci wasu ayoyi kamar ayar Wilaya

(انما ولیکم الله و رسوله...) 

Ko ayar Ikmaud Deen ba

 (الیوم اکملت لکم دینکم ...)

 a matsayin mafificin shaida kyawawan halaye falala mai muhimmanci ga Imam Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba A'a, ya ambaci ayar Mubahlah da hujjar cewa Amirul Muminin, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a cikin wannan ayar, shi ne ruhin Annabi a matsayin mafi girman falalar Alkur'ani ga Imam Ali As.


A bisa hujjojin sama da Imami na 8 cikin jerin Imaman shiriya As da ya anbata Imam Amirul Muminina shi ne ruhi da ran Annabi, idan kuma Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne mafificin Annabin Allah, to Amirul Mu’u minin kuma shi ne mafificin halifan Annabi, don haka haqqin al’ummar musulmi ne limaminsu ya zama mafificin mutum bayan Annabi, kuma imamanci da shugabanci ya kasance a hannun mafificin mai kyawun halaye mafi adalci.


Girman Mubahalah ya sanya ta a matsayin daya daga cikin mafi wanzuwar al'amura a tarihin Musulunci, amma bawa batun hakkinsa ba na yi bayanin gaskiyar hakikanin da matsayin da ke ciki ba kamar yadda ake bukata.


A shekarun baya-bayan nan dai jama’a da ‘yan Shi’a a sassa daban-daban na duniya sun maida hankali da bada muhimmnaci wajen gudanar da bukukuwan zagayowar ranar babban idi na Ghadir, amma ta hanyoyi daban-daban da suka hada da gudanar da shi har karshen kwanukan goma na wilaya bayan wucewar Idul Ghader. Amma ranar Mubahalah da ita take a matsayin hujja mai ingancin a Musulunci da wilayar Amirul Muminin da daukaka ga Shi'a ba su mai da hankali wajen tunawa da janyo hankalin mutane a kafafen yada labarai ba, yayin da girma da daukaka. Muhimmancin wannan rana da bayyanar da ilimin da falala da ayyukan wannan Idi su ma suna bukatar karin sabunta su.


.................................