Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

6 Yuli 2023

11:07:08
1377561

Akwai Kebantattu Halaye Na Imam Ali (a.s) Guda 150 A Ziyarar Ghadir

Ayatullah Ramadani: Ahlul Baiti (A.S) Su Ne Ginshikin Hadin Kan Musulmi

Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya bayyana cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya kwadaitar da musulmi a cikin Hadisin Abubuwa biyu masu nauyi da su kiyaye Alkur'ani da aiki da shi, da riko da Ahlul Baiti. (S.A.W) kamar yadda ake la'akari da wannan batu shi ne mafi girman wasiyarsa (SAW).

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan cika kwanaki masu albarka na goma na Wilayah na shugabantar da Imam Ali As da kuma bukukuwan mafi girman Idin Sallah, Ayatullah Reza Ramadani, Babban Sakatare na Majalisar Ahlul Baiti (A.S), ya halarci wani biki da aka gudanar a birnin Karachi, inda ya gabatar da jawabi.


Ayatullah Ramadani ya yi ishara da nauyin da doru akan masu Tabligi da malaman addini a fagen isar da sako, in da ya ce: Mai girma Ayatullah Bahjat, Allah Ya yi masa rahama, ya kasance yana cewa ku masu tabligi ku yi kokarin kun sanar da Allah ga mutane. Nietzsche ya yi kokari a zamaninsa don ya shafe Allah daga zukatan mutane, amma idan Allah bai kasance rayuwar mutane ba, to rayuwarsu ta kasance a banza kenan marar anfani.


Da yake jawabi ga masu Tabligi, babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (AS) ya ce: Allah mai albarka ya dora muku amana mafi girma, wato addini da Sharia, domin ku koye shi hakikanin koyo sannan ku koyar da shi.


Shugaban ya yi ishara da ranaku goma masu albarka na wilaya da muhimmancin Hadisin Abu biyu masu nauyi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya kwadaitar da musulmi a cikin Hadisin akan Abu biyu masu nauyi da su kiyaye Alkur'ani da aiki da shi, da yin riko da Ahlul Baiti (A.S) kamar yadda ake ganin shi ne mafi girman umarninsa (SAW), don haka Imam Khumaini (Allah Ya jiqansa) tare da la'akari da wannan muhimmanci da wajibcinsa ya kasance wannan hadisin Nauyayay guda biyu shine Abu na farkon abin da ya yi wasiya da shi a cikin wasiyyarsa.


Babban magatakardar majalisar ta Ahlul-Baiti (a.s) ya yi ishara da muhimmancin shiryar da mutane, ya kuma kara da cewa: Allah madaukakin sarki shi ne mai kula da lamarin shiriya a cikin tsarin samuwar da wanzuwarta, da kuma tsarin tafiyar da al'amuran shari'a kuma ya aiko da annabawa don shiryar da mutane zuwa ga hanya madaidaiciya, kuma ya saukar da littattafai na Ubangiji don cimma wannan manufa, da kuma cewa hankali yana shiryar da mutum zuwa ga annabawa da shari'a don mutum ya kai ga farin ciki, kamar yadda bamu yarda da tsagwaron hankali ba kadai. Domin hankalinmu shi ne "hankali ne na dabiar halitta".


Jagoran ya tabo batun zaluntar Ahlul Baiti (A.S), sannan ya ci gaba da cewa: me ya faru har ya zamo bayan wafatin Manzon Allah Sawa da shekaru talatin aka daga takardun Alkur'ani bisa masu, kuma shekaru 50 bayan tafiyarsa, za a daga Kur'ani mai magana a gefen korama? Duk wadannan matsalolin suna faruwa ne saboda rashin kula da umarnin Manzon Allah (SAW) don haka Imam Husaini (AS) ya yi shahada don al’umma ta fita daga cikin rudanin bata, kamar yadda Imam Amirul Muminin Ali (A.S) yana jin radadi ga wadanda suke rayuwa cikin jahilci.


Babban Farfesan darussa a makarantar hauza ta ilimi ya sanya jahilci a mafi girman cuta ga mutane, ya kuma kara da cewa: Ba mu yi tawassuli da Ahlul Baiti (SAW) ba hakikanin tawassuli, kamar yadda ba mu yi tuntuntuni a kan Alkur’ani ba; Kur'ani haske ne, kuma dole ne mu yi tunani a kan Alkur'ani tare da karanta ayoyin wannan littafi na sama. Tunda Alkur'ani ya nemi mu yi tunani a kan ayoyinsa, sannan mu gabatar da kanmu ga Alkur'ani, daga wannan mahangar ne muka yi la'akari da cewa muna masu fuskanto kwanaki na ta'aziyya da kuka ga Jagoran Shahidai Imam Husain As, dole ne watan Muharram da Ashura mai alfarma ya zama dalilin gyara ga mutum da ayyukansa a cikin al'umma.


Dangane da matsayi da kimar Alkur'ani, Jagoran ya ce: Alkur'ani ya zo da nufin mutum ya kai ga gaskiya, kuma shi ne mai cetonmu duniya da lahira. Harshen Kur’ani shi ne harshen hankali da ilhami. Alkur'ani mai ceto ne a ranar sakamako da rokon Allah mai tsarki ya tabbata a gare shi, ga wadanda suka yi riko da shi kuma suka kiyaye shi, don haka wajibi ne mu kara saninsa fiye da kowane lokaci. Ahlul Baiti (A.S) su ne ainihin masu magana da Alkur'ani, kuma dole ne mu fahimci Alkur'ani ta hanyarsu, kuma mu dauki ilimin Alkur'ani daga gare su, don haka dole ne mu fahimci Alkur'ani. 'a cikin harshen Ahlul Baiti (A.S); Alkur’ani mai girma ya bukaci mu saurara kuma mu kula da fadin Manzon Allah (SAW) domin fadin Alkurani cewa: “Duk abin da Manzo yazo maku da shi, ku karba, abin da ya hane ku, ku kaurace masa”.

«ما آتاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَ ما نَهاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا».


Kuma babban sakataren Ahlul-baiti ta duniya (a.s) ya kara da cewa: Ahlul-baiti (a.s) sune ginshikin hadin kan musulmi, kuma gaskiya da hakikaninta suna garesu imamai (a.s) da Iliminsu Ahlul Baiti (a.s) don haka mun yarda cewa gaskiya tana tare da Ali, Ali yana tare da gaskiya, gaskiya tana tare da shi duk inda ya ke, kuma idan muna son sanin sifofin Amirul Muminin. (A.S) kuma mu saurari darajojinsa, wajibi ne mu koyi su kuma mu saurare su ta harshen Ahlul-baiti (A.S), kuma kamar yadda Imam Al-Hadi (a.s) ya ambata halayr 150 na Imam Ali (a.s). (AS) a ziyarar Ghadiri.


Kuma game da manufar masu Tabligi ya ce: Dole ne masu Tabligi su horar da kansu ta yadda za su iya daukar abin da aka dora musu, su sadar da addini, domin mu koyi abin da ya shafi addini daidai yadda ya kamata mu koye shi.


Dangane da kona kur'ani mai tsarki a kasar Sweden, Ayatullah Ramadani ya ce: Me ya sa gwamnatin kasar Sweden ta ba da izinin kona Alkur'ani mai girma da nufin cutar da musulmi biliyan 4 masu bin addinin Musulunci da kuma addinan Ubangiji? Dokar ‘Yancin fadin albarkacin bakinsa dalili ne na yin haka. An yarda a kona Alkur’ani; Domin kuwa Alkur'ani yana da matsayi mai girma a tsakanin musulmi, kuma musulmi da kasashen musulmi za su dauki kwararan matakai na hana aiwatar da wannan danyen aiki da mummunan aiki na mahukuntan kasar Sweden.


Yana da kyau a lura cewa Hujjatul-Islam Morsali, karamin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Karachi Mr. Nourian, shugaban majalisar al'adu Dr Talebi Nia, babban sakataren majalisar malaman Shi'a a Pakistan Hujjatul-Islam Shabbir Hassan Maisami, da manyan malamai da masu wa'azi kusan 200 ne suka halarci wannan tarukan, Ahlul Baiti (AS).


A farkon wadannan tarukan, bayan karanta ayoyi na zikiri mai hikima na Kur'ani, daya daga cikin ma'aikatan mimbarin Husaini da Ahlul Baiti (a.s) ya rera wakoki na yabon Amirul Muminin (a. na Eid al-Ghadir, in da Hujjatul-Islam Maisami ya mika godiyarsa gababban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (A.S) bisa ziyarar da ya kai Pakistan, a cikin gajeren jawabinsa.


A nasa bangaren, Talbi Niya ya mika godiyarsa ga Ayatullah Ramadhani da tawagarsa, tare da bayyana ayyukan majalisar al'adun kasar Iran a wannan kasa.


..........