Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

4 Yuli 2023

07:56:07
1377039

Kwamandan Yahudawan Sahyoniya: Hizbullah Ita Ce Babban Hatsari A Gare Mu

Tsohon shugaban hukumar leken asirin soji na gwamnatin sahyoniyawan a wani jawabi da ya yi na tabbatar da karfin soji na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya dauki wannan yunkuri a matsayin babbar barazana ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Amos Yedlin tsohon shugaban hukumar leken asirin soji na gwamnatin sahyoniyawan kuma kwamandan ajiyar sojojin wannan gwamnati a cikin wani jawabi da yayi game da hakan ya bayyana cewa: Babbar barazana ga Isra'ila a yau tana cikin arewacin kasar wato (Hizbullah).

Da yake amincewa da karfin soja na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, ya kara da cewa: Hizbullah tana da karfin dakaru mai tsari a yakin na gaba.

Yayin da yake ishara da irin karfin da kungiyar Hizbullah ke da shi a yakin da ke tafe, Yadlin ya ce: Ana sa ran cewa a wannan yakin Hizbullah za ta tsallaka kan iyaka da dakarunta, kuma ba za mu iya tsallakawa kan iyaka ba.