Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

4 Yuli 2023

07:29:38
1377029

Wuce Gona Da Iri Na Yahudawan Sahyoniya A Ci Gaba Da Kai Wa Falasdinawa Hari

Mayakan Sahyoniyawa Sun Sake Kai Hari Sansanin Jenin

Kafofin yada labaran Falasdinu sun ba da rahoton harin bam da aka kai a wani yanki a sansanin Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan da safiyar Talata.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Mayakan yahudawan sahyoniya sun kai hari a yankin "Al-Damj" da ke sansanin Jenin.

Ana gudanar da wannan harin bam ne a lokaci guda tare da tsananta rikicin da ke tsakanin dakarun gwagwarmayar Palastinawa da sojojin yahudawan sahyoniya.

Majiyoyin cikin gida sun kuma bayar da rahoton cewa, an ji karar fashewar wasu abubuwa a sansanin Jenin bayan wannan tashin bam.