Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

3 Yuli 2023

15:17:49
1376835

Paparoma Ya Nuna Ƙyama Da Kona Kur'ani

Duniya Na Bukatar Masu Kira Zuwa Ga Zaman Lafiya

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Fafaroma Francis, yayin da yake nuna fushinsa kan yadda ake yawan wulakanta wurare masu tsarki na Musulunci, ya bayyana irin wadannan dabi'u a matsayin wanda ake kyamatarsu da kuma yin tir da su.

Shugaban darikar Katolika na duniya ya ce: Ina jin haushi da kyama da wadannan halaye. Duk wani littafi da ya ke na ansaukar da shi daga sama kuma ga mabiyansa ya zamo abun tsarkakewa to ya kamata a girmama shi ga waɗanda suka yi imani da shi su ke girmama shi.

Paparoma Francis ya jaddada cewa: Bai kamata 'yancin fadin albarkacin baki ya zama uzuri na wulakanta wasu ba, kuma barin hakan abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma abin Allah wadai ne.

Yayin da yake mai nuni da cewa manufarmu ita ce mu mayar da fahimtar addini zuwa hadin kai, 'yan uwantaka da ayyukan alheri na zahiri, ya jaddada cewa: makomar hadin gwiwa tsakanin addinai ta ginu ne a kan tsarin mutunta wasu bangarr bisa gaskiya.