Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

2 Yuli 2023

08:14:45
1376515

Musulman Kasar Georgia Sun Yi Allawadai Da Tozarta Alkur'ani

Bayan wulakanta kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Sweden "Haji Gurban Morguzov" masanin addinin Islama na kasar Georgia ya bayyana cewa: Musulman kasarsa sun yi tir da wannan mummunan lamari.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Ya ci gaba da cewa: “Abin bakin cikin shi ne a cikin kwanakin Idin karamar Sallah, makiya Musulunci da Musulmi da suka dade ba su daina munanan ayyukan da suke yi ba, kuma abin bakin cikin su ma sun sake cin zarafin littafin Alkur’ani mai girma, lamarin da ya kasance mummunan lamari. " Wannan dai ya faru ne a wata kasa da ake ganin al'ada ce a tsakiyar nahiyar Turai ta wani dan asalin kasar Iraki wanda ba ya da addini kuma bai yarda da Allah inda abun ya faru gaban 'yan sanda.