Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

1 Yuli 2023

12:05:12
1376317

Halin Da Mahajjatan Ke Ciki A Saudiyya

Amir Abdullahian ya bayar da bayani dangane da halin da mahajjata ke ciki na baya-bayan nan a Baitullah Al-Haram

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A cikin wannan tattaunawa ta wayar tarho, ministan harkokin wajen kasarmu ya bayyana jin dadinsa da yadda alhazan kasar Iran da sauran alhazan ke gudanar da aikin Hajji ba tare da matsala ba, kuma mun ji dadin samu masaniya ga hali mahajjata a kasar Wahayi.

Wakilin Jagora a aikim hajji Hujjatul Islam wal-Muslimin Sayyid Abdul Fattah Nawab, masanin fikihu ya bayyana jin dadinsa da yadda ake gudanar da aikin Hajji da kuma yadda ake gudanar da ayyukan ibada har zuwa yanzu, yanayi na baya-bayan nan da kuma yanayin da ya shafi mahajjatan kasar Iran inda ya bada wasu shawarwari ga alhazai mafi kyawu da saukin gudanar da ayyukan Hajji da ayyukan ibada da mahajjatan Baitullahi Al-Haram a shekaru masu zuwa tare da fatan za a la'akari da su.