Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

1 Yuli 2023

11:38:54
1376313

Saudiyya Dai Ba Ta Yarda Gwamnatin Sahyoniya Ta Halarci Taron UNESCO Ba

Kafofin yada labaran kasashen yammacin duniya sun rawaito cewa, Saudiyya ba ta bari wakilan gwamnatin sahyoniyawan su halarci tarukan hukumar raya ilimi da kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO).

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A cikin rahoton an kawo cewa, har yanzu Saudiyya ba ta sanya hannu kan takardar da wakilan gwamnatin sahyoniyawan za su halarci taron UNESCO na watan Satumba a birnin Riyadh ba.

Jami'an diflomasiyya da manyan jami'an gwamnatin yahudawan sahyuniya sun bayyana cewa Saudiyya ba ta yi magana musamman ga gwamnatin sahyoniyawan kan kin sanya hannu kan wannan takarda ba, amma sun bayyana karara cewa Isra'ila ita ce babbar matsalar.