Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

26 Yuni 2023

06:47:51
1375429

Lapid Yayi Gargadi Game Da Rugujewar Isra'ila Da Rudanin Tattalin Arziki

Lapid ya koka Game da yiwuwar barkewar jayayya da rugujewar Isra'ila cikin rudanin Tattalin Arziki





Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Yair Lapid tsohon firaministan Isra'ila ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: "A cikin kwanaki masu zuwa, ministan shari'a na Isra'ila, Yario Levin, da Simsha Rotman, wakilan jam'iyyun gamayyar kasa da kasa, za su yi iya kokarinsu don kawar da yiwuwar dawowar mu zuwa gidan shugaban Isra'ila, Isaac Herzog, maimakon Isra'ila" don su jawo yin jayayya cikin Israila, wanda dukanmu mun san farashin abinda hakan zai jawo

Ya kara da cewa: Za a samu tabarbarewar tsadar tattalin arziki, tsadar rayuwa za ta karu, harkar tsaro zai tai matukar illata, kasashen duniya za su juya mana baya, al'ummar Isra'ila za ta durkushe.