Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

26 Yuni 2023

06:27:32
1375419

Nasihohi 3 Da Imam Muhammad Baqir (As) Yayi Ga ‘Yan Shi’a Domin Samun tsira Daga Cutarwa

Imam Muhammad Baqir (a.s.) yana fada a cikin ruwaya cewa Allah bai ba da wani izini ko wata dama ta sassauci ga yin abubuwa guda uku ba kuma akwai bukatar gaggauta aiwatar da su a cikin Al'umma da zamantakewa.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - bisa ranar tunawa da shahadar Imam Muhammad Bakiril Ulum Imami na biuar cikin jerin limaman shiriya da Annabi Sawa ya barwa Al'ummarsa sun kawo maku wasu daga cikin gwalagwalan kalaman wannan Imami na koyarwa ga alumma lokacin da yayi lokacin rayuwarsa.

Imam Muhammad Baqir (a.s.) yana fada a cikin ruwaya cewa Allah bai ba da wani izini ko wata dama ta sassauci ga yin abubuwa guda uku ba kuma akwai bukatar gaggauta aiwatar da su a cikin Al'umma da zamantakewa.

Da wata ma’ana kuma akwai salon rayuwa ne wadanda wannan limami mai tausayi ga Al'umma suka tsara mana, don kada ‘yan Shi’a su cutu a wadannan wurare guda uku:

1- Amincewa da rikon amana ga mutumin kirki da mara kirki: Rikon amana ba wai don dukiya da kadara ce kadai ba, a’a da’ira ce mai fadi wacce ta hada da amana ta ruhi kamar Al-Qur’ani da lamurran addini da sauransu.

2- Cika Alqawari: daya daga cikin muhimman darussa na mazhabar shi’a shi ne kiyaye alkawari ko da a cikin ciniki ne saboda tabarbarewar kasuwa; Misali, a zamaninmu, wani lokaci ana yin aure da alkawuran da ba su kirguwa ba, amma namiji ko mace suna karya alkawari a tsakar hanyar rayuwarsu, yayin da ya zama dole su tsaya kan alkawarinsu.

3- Girmama iyaye yana daga cikin manya-manyan al'amura da suke kaiwa ga kyakkyawan karshe; an ruwaito girma da tsarkin iyaye da yawa a cikin ruwayoyi na tarihin limamai, musamman masoyin Manzon Allah (SAW). A zamanin Manzon Allah (S.A.W) wani matashi Bayahude yana da sha'awar Musulunci sosai, kuma a lokacin wafatinsa yazo Manzon Allah (saww) sun zo bakin gadon wannan matashin, don shiga Musulunci sai wannan saurayi ya kalli wannan mahaifinsa, sai yaga uban bai nuna yardar shi ba na ya furta kalmar shahada, hakanan ya rasu ba tare da yayi kalmar shahada ba.