Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

22 Yuni 2023

13:04:09
1374746

Kan'ani: Gwamnatin Yahudawan Sahyoniya Tana Gajarta Rayuwarta Ne

Gwamnatin Yahudawan Sahyoniya Tana Gajarta Rayuwarta ta Hanyar Ci Gaba Da Aikata Laifukan Da Mugunta

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Nasser Kanani ya rubuta a shafinsa na Twitter inda ya yi ishara da irin abubuwan da suke faruwa a Palastinu a baya-bayan nan da kuma tsayin daka da gwagwarmaya kungiyoyin gwagwarmaya suke yi suna masu fuskantar wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawa inda ya rubuta wata karin magana dake cewa: duk wanda ya shuka iska to zai girbi guguwa. Wato (abunda ka shuka shi zaka girba)

Juriya da tsayin daka da gwagwarmaya su ne martanin da al'ummar Palastinu ke yi na dabi'a kuma na halal a kan ta'addancin mamaya da wariyar launin fata, kuma al'ummar Palastinu da ake zalunta masu tsayin daka ba za su bar ta'addancin da aka tsara da kuma muggan ayyukan yahudawan sahyoniya ya ci gaba ba.

"Gwamnatin yahudawan sahyoniya tana gajarta rayuwarta tare da ci gaba da aikata laifuka da mugunta."