Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

22 Yuni 2023

12:39:22
1374735

Falasdinawa 3 Sun Yi Shahada A Harin Da Jiragen Yakin Gwamnatin Sahyoniya Suka Kai

Majiyoyin yada labarai sun rawaito cewa jiragen yakin yahudawan sahyoniya sun kai hari kan wata mota a garin Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan, inda Falasdinawa uku su kai yi shahada a wannan harin ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Kungiyar Relief and Rescue Palestine ta sanar da cewa an gano gawarwaki mutane uku a cikin wata mota da jirgin Isra'ila mara matuki ya auna.

Sojojin Isra'ila sun tabbatar da wannan rahoto tare da sanar da cewa, a wannan harin, an kai hari ga wata mota dauke da makamai masu linzami da dama.

Jaridar ‘Yediot Aharanot’ ta yahudawan sahyuniya ta yi ikirarin cewa jiragen yakin wannan gwamnatin sun kai hari kan wata mota da mutanen da ke cikinta suka yi harbi a daya daga cikin shingayen binciken gwamnatin sahyoniyawan da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan.