Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

21 Yuni 2023

02:43:45
1374393

Darussa guda biyar Da Zamu Koya Daga Rayuwar Imam Ali As Da Sayyidah Zahra'u As

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - Yana Ci Gaba Da Taya Ku Murnar Ranar Masoya Bisa Munasara Auren Imam Ali As da Sayyidah Zahra'u As

Ni daga wannan rayuwar da ta fara daga wannan daren Ma'ana farkon daren auren Imam Ali As da Sayyidah Zahra'u As inaso na tunatar da ku darussa guda biyar da zamu kowa daga wannan Rayuwar ta su: 

Darasi na farko shine: shine: Tushen asali ginshiki na rayuwar wadannan manyan mutane shine an ginata ne bisa yardar Allah da yi masa biyayya.

Darasi na biyu shine: sassaukar rayuwa dake tsakaninsu, domin yayin da sayyidah Fatimah tazo gidan Imam Ali Amiral Mu'uminen As sai hawaye suka kwaranyo a idanuwarta, sai ya tambayeta yake masoyita Fatimah shin dalilin kukanki shine kuncin rayuwa? Ko kina da wanin abun rayuwa da yayi karanci a rayuwarki? sai tace ko kadan babu, ya Amiral Mu'umineen na tuna cewa tabbas akwai ranar da zan tafi kabari daga wannan gidan nawa ne. 


Darasi na uku shine: tushen ginshiki dake tsakanin Sayyidah Zahra'a da Imam Ali As Shine girmama Juna, ku duba irin maganganun da suke furtawa juna irinsu raina fansar rayinka ne, kaina fansa ne agareka, idan har ka kasance acikin Alkhairi to na kasance tare dake cikinsa, kana da shi ko baka da shi, wannan abu ne mai muhimmanci sosai!.


Darasi na hudu shine tushen: Soyayya, nuna kauna saboda hakane manzon Allah Sawa ya ke cewa: idan kanason matarka ka fada mata cewa kana sonta. 


Darasi na biyar shine: shine tushen ginshikin hakuri da juriya, akwai ruwayar da take cewa idan mace tace da mijinta ni ban wani ga Alkhairi a gidanka ba duk abunda yayi na ibada sallah azumi komai da komai zai lalace ya zamo ba shi da ladansu