Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

20 Yuni 2023

14:59:36
1374330

Muna Taya Al'ummar Duniya Musamman Musulmai Murnar Da Zagayowar Ranar Ma'aurata

Murnar Zagayowar Ranar Auren Imam Ali Da Sayyidah Fatima Az- Zahra'u (As)

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - Na Taya Al'ummar Duniya Musamman Musulmai Murnar Da Zagayowar Ranar Ma'aurata Ta Duniya

Lamarin Auren Imam Ali da Fatima al-Zahra, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, na daga cikin abubuwan da suka faru a shekara ta 2 bayan hijira, inda 'yan Shi'a ke gudanar da bukukuwan daurin auren Uwargidarmu Az-Zahra da Imam Ali (As) a ranar farko ga watan Zul -Hijja kamar yadda ake kiran wannan aure da auren fitulun haske guda biyu, kuma ranar tana da matukar muhimmanci a gare su dama al’umma gaba daya; Domin su biyun, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, suna daga cikin manya-manyan mutane kuma fiyayyun halitta bayan Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa, kuma imamai ma'asumai, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su sune 'ya'yan da aka samu ta wannan aure.


Wanda Ya rubuta: Shafiu Kabiru


Haka kuma wannan aure yana nuni da matsayin Imam Ali mai tsira da amincin Allah a wurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa, kasancewar babu wani makamancinsa Domin ya auri 'yarsa Sayyidah Fatima da amincin Allah su tabbata a gare ta.


Riwayoyin Dangane Da Wannan Aure:

Imam Ali (a.s) yana da shekara ashirin da hudu a shekara ta 1 bayan hijira, kuma Sayyidah Fatima al-Zahra (a.s) ta kai shekara tara a lokacin bisa dogaro da riyawar haihuwarta a shekara ta biyar bayan aiko Manzo SAWA. Shi kuma Imam Ali (a.s) ya yi niyyar auren Fatima saboda kyawawan halaye nata da falalarta, amma bai iya ambata hakan ga Annabi ba. An ruwaito cewa Sa’ad bin Mu’az ya yi dan tsakani ga Ali da Annabi kan lamarin, kuma lokacin da Sa’ad ya tambaye shi dalilin da ya hana neman aurenta ga Manzon Allah, sai ya amsa yana mai kin son fadin dalili: “kana ga zan iya samun jarumtar nemanta daga manzon Allah? Wallahi da a ce baiwar sa ce ba zan iya neman aurenta daga wajensa ba. Sai Sa’ad ya yi batun ga Manzon Allah, sai Manzon Allah ya ce masa: Ka ce masa ya yi, ni kuwa zan aikata.


Kuma an samo labari daga gare shi, ya ce, ya zo wurin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam) ya nemi auren ‘yarsa Sayyidah Fatima, sai Annabi ya ce masa akwai mutanen da suke neman aurenta, ya kuma ba shi labarin nuna kin hakan da ta yi inda ya gani a fuskarta a lokacin da ya sanar da ita bukatarsu, sai ya anbata mata bukatar neman aurenta da dan uwansa ya gabatar, yana mai ce mata: Ali Ibn Abi Talib, kin san danginsa, da falalarsa, da Musuluncinsa, domin na roke Ubangijina. ya aurar da ke zuwa ga mafificin halittunsa kuma mafi soyuwa a gare shi. Sai tayi shiru bata kawar da fuskarta ba, kamar yadda Annabin Rahama SAWA bai ga kin hakan a fuskarta ba, sai ya tashi yayi Kabbara. Kai tsaye sai ga Mala’ika Jibrilu ya zo ya tabbatar da hadin auren.


Haka nan kuma an ruwaito cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya yiwa Imama Ali As bushara a majalisin da ya nemi auren Sayyida Zahraa (AS), cewa: Allah Madaukakin Sarki ya aurar da su a sama kafin ya aure su a doron kasa.


A wata ruwayar kuma daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “ a lokacin da nake sallar Asuba a ranar Juma’a, sai na ji karar mala’iku, sai ga masoyina Jibrilu, tare da shi sahu saba’in na mala’iku suna masu rawani da kayan ado na ce: Menene wannan sautin farinciki da murna sama, ya kai Jibrilu?! Ya ce: Ya Muhammadu! Allah Ta’ala ya duba kasa, sai ya zabi Ali daga cikin maza wanna duban, kuma daga cikin mata ya zabi Fatima, sai ya aurar da Fatima ga Ali. Sai Fatima (a.s) ta daga kanta ta yi murmushi... ta ce: Na gamsu da abin da Allah da Manzonsa suka yarda da shi.


Anas ya ce: sai ga Ali ya fuskanto sai Annabi (SAW) ya yi murmushi, sannan ya ce: “Ya Ali, Allah Ya umurce ni da in aurar da kai ga Fatimah, domin ya aurar maka da ita kan mithkal din azurfa dari hudu idan ka yarda. Sai Ali ya ce: Na gamsu ya Manzon Allah... Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Allah Ya yi muku albarka gareku da cikinku Ya sanya ku cikin farin ciki, ya fitar da alheri daga gare ku”.

Anas ya ce: Wallahi akwai alheri mai yawa da ya fita daga gare su.

Ruwayoyin Neman Aurenta Daga Sahabbai:


Akwai ruwayoyin da aka samu ta littattafan Ahlus Sunnah da suka yi magana a kan neman auren da Sahabbai ga Fatima (AS), yayin da Annabi (SAW) ya bai maraba da neman ba, ya aurar da ita ga Imam Ali (AS);

Ga Ruwayoyin Kamar Haka:


Ibnul Asir ya ruwaito da isnadinsa daga Abu Ishak daga Harith daga Ali ya ce: Abubakar da Umar sun nemin auranta - ma'ana Fatima - sun yi magana da Manzon Allah (SAW) - amma Sai Manzon Allah (SAW) ya ki su, sai Umar ya ce: Kai ne ka cancance ta ya Ali, sai na ce: Ba ni da komai face garkuwata na jinginar da ita. Sai Manzon Allah (SAW) ya aurar da ita ga Fatima, da jin labarin haka sai Fatima ta yi kuka, sai ya ce: sai Annabi SAWA ya shiga wajenta yace: me ya sanya ki kuka ya Fadimah? Wallahi na aurar dake ga wanda yafi su ilimi kuma yafi su hakuri da juriya, kuma na farkonsu a musulunta.


Daga Buraidah ya ce: Abubakar ya nemi auren Fatima, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Yarinya ce, kuma ina jiran a saukar da hukunci dangane da lamarinta. Sai Umar ya gamu da Abubukar, sai ba shi labarin abun ya faru, sai ya ce: bai amsa maka ba ko, sai Umar shima ya nemi aurenta shima Annabi bai aminta ba.


Kuma an samu ruwaya daga Abdullahi dan Buraidatah daga babansa ya ce: Abubakar da Umar sun nemi auren Fatima, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: (Yarinya ce), sai Ali ya nemi aurenta , sai Annabi SAWA ya aurar da ita ga shi. Ahmad bin Hanbal da Nisa’i Hakim da Ibn Sa’ad ne sukafitar da hadisin.

Yadda Auren Ya Gudana:

Manzon Allah (SAW) ya ce:

“ Wannan Jibrilu ne yake gaya mani cewa Allah ya aurar da Fatima gareka, kuma mala’iku dubu arba’in suka shaida aurenta, sai ya yi wahayi zuwa ga bishiyar albarka ta (Duba): data yayyafa musu lu’ulu’u da yakutu, sai ta yayyafa musu lu’ulu’u da yakutu. Sai matayen Hurul Iin suka garzaya zuwa gare ta, su tãra a cikin marafai na lu'ulu'u da yaƙũtu, sai suna yin kyauta da shi tsakãninsu har zuwa Rãnar Alkiyãma.


Al-Qandouzi Al-Hanafi, Yanabi’ul Mawaddah, Mujalladi na 2, shafi na 124.

Ibn Abi Al-Hadid ya ce: Kuma aurarwar da Annabi yayi wa Ali da Fatimah bai kasance ba sai bayan da Allah Ta’ala ya aurar da su a sama da shaidar mala’iku.

Kuma daga Ibn Mas’ud, daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah ya umurce ni da in aurar da Fatima ga Ali.

Kuma an karbo daga Umar Ibn Khattab ya ce: “Jibrilu ya sauko ya ce: ‚Ya Muhammadu! Allah ya umurce ka da ka aurar da ‘yarka Fatima ga Ali”.


Ba Don Ali Ba, Da Fatima Ba Za Ta Samu Daidai Da Ita Ba (Tsaranta)

Ya zo a cikin ruwaya cewa Annabi (SAW) ya zo wajen Fatima (AS)... sai ya ce mata daga cikin abin da ya ce: “Wallahi da a ce a cikin iyalaina (mutanen gidana) akwai wanda ya fishi; Da Ba zan aurar da ke gare shi ba, kuma ba ni na aurar dake ba saia dai Allah ne y aurar dake”.

Kuma a cikin wata ruwayar: “Da Ali bai kasance ba (ba a halicce shi ba) (kuma an ruwaito: bai aure ta ba), da Fatima ba ta samu tsara ba”.


Neman Auran Da Al’ummar Musulmi Suka Shaida:

An karbo daga Ummu Salama da Salmanul Farsiy da Jabir cewa: “Lokacin da Manzon Allah ya so ya aurar da Fatima ga Ali (a.s), sai ya ce masa: (ka fita ya Abal Hassan, zuwa masallaci, domin Zan fito a bayanka, kuma zan aurar da kai a gaban mutane, kuma zan ambaci falalarka da abin da zai faranta idanunka...).


Ali (a.s) ya ce: (Wallahi ba mu kai tsakiyarsa ba har sai da Manzon Allah ya riske mu, kuma fuskarsa tana farin ciki da annashuwa).


Sai (SAW) ya ce: (Ina Bilal?).

Sai ya amsa da sauri ya ce: gani a hidimarka, kuma na yarda da kai ya Manzon Allah.

Sai ya ce: (Ina Miqdad?).

Sai ya amsa da cewa: gani wajen hidimarka ya Manzon Allah.

Sai ya ce: (Ina Salmanu?).

Sai ya karba masa da cewa: ina shirye wajen hidimarka ya Manzon Allah.

Sai ya ce: (Ina Abu Dharr?).

Sai ya karba masa da cewa: gani shirye wajen hidimarka ya Manzon Allah.

Da suka bayyana a gabansa, sai ya ce: ((Ku tafi gaba dayanku, ku tsaya a gefen garin, ku tara Muhajirai, da Ansar da musulmi).

Sai suka tafi zuwa ga umurnin Manzon Allah (S.A.W)..., sai Manzon Allah (SAW) ya matso ya zauna a kan mafi kololuwar mataki na mimbarinsa, sai masallaci ya cika makil da iyalansa, sai Manzon Allah (S.A.W). Allah (S.A.W) ya mike, ya gode ma Allah, ya yabe shi... Kuma ya ambaci batun neman auren, har sai da ya ce - : (Kuma Allah Ta’ala ya umarce ni da in aurar da ‘yata Fatima ga dan uwana, kuma dan dan uwana, kuma mafi kusanci da ni ga mutane Ali Ibn Abi Talib, domin ya aurar da su a sama da shedar mala’iku, kuma ya umarceni da in aurara da su a doron kasa, kuma shaidar daku akan hakan).

Sai Manzon Allah (SAW) ya zauna, sannan ya ce: (Tashi ya Ali – don haka ka nemawa kanka auren...).

Sai Ali (a.s) ya fara da cewa: (...Aure yana daga abin da Allah Ta’ala ya yi umarni da shi, kuma ya yi izini, kuma wannan majalasin namu yana daga abin da Ya hukunta kuma Ya yarda da shi, kuma wannan shi ne Muhammad bin Abdullahi... Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa’alihi, ya aurar mini da ‘yarsa Fatima, akan sadaki dirhami da dinari dari hudu, kuma na yarda da haka, don haka ku tambaye shi kuma ku shaida).


Sai musulmi suka ce: Ka aurar masa ​​ya Manzon Allah?


Sai ya ce: (Na’am).

Sai Musulmi suka ce: Allah ya yi albarka garesu da kansu, kuma ya hada kawunansu.