Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

18 Yuni 2023

15:05:10
1373868

Hanyoyin Kasa Da Hizbullah Labanon Tayi Karkashin Matsugunai Da Cibiyoyin Tsaro Na Gwamnatin sahyoniyawa

A yayin da take tabbatar da karfin soji da tsaro da dabarun kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, rahoton cibiyar binciken yahudawan sahyoniya "Alma" ta rubuta game da sabbin karfin da wannan yunkuri yake da shi: Hizbullah ta bunkasa karfinta na karkashin kasa a kasar Lebanon, wanda ya hada da jerin ramuka da ke kusa da kan iyaka tare da yankunan da aka mamaye (Isra'ila).

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Wannan cibiya ta bayyana a cikin rahotonta cewa: Daga cikin abubuwan mamaki da Sayyid Hasan Nasrallah ke shiryawa don fuskantar futo na futo a nan gaba, akwai ramukan da ake tonawa a karkashin matsugunan Isra'ila ko kuma cibiyoyin tsaro. Wamda Fashewar waɗannan ramukan na iya lalata garin ko wurin gaba ɗaya. Babu wani takamaiman bayani game da irin wadannan ramuka, amma muna da wuya mu yarda cewa Hizbullah ba za ta yi amfani da irin wannan damar ba a yakin na gaba.