Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

16 Yuni 2023

14:30:57
1373494

An Harbo Wani Jirgi Mara Matuki Dauke Da Makamai A Kan Iyakar Syria Da Jordan

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin kasar Jordan ta fitar ta bayyana harin da aka kai kan wani jirgi mara matuki dauke da makamai daga kasar Siriya a kan iyakar kasar da wannan kasa.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, a cewar wannan rahoto, wata majiyar soji ta bayyana cewa, dakarun tsaron kan iyakoki tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro da na soji, sun lura da wani yunkuri na tsallakawa wani jirgin mara matuki daga Syria zuwa kasar Jordan tare da harbo shi a cikin yankin na Jordan.

A cewar wannan majiyar sojan, jirgin mara matuki na dauke da makamai daban-daban da aka gano bayan harbo shi.

Majiyar sojan ta ce dakarun kasar Jordan za su tunkari duk wata barazana da ke tunkarar yankunan kan iyaka da karfi da kuma azama.