Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

16 Yuni 2023

14:23:50
1373493

An kama Wanda Ya Kai Harin Ga Wani Malami A Tehran

Bayan harin da wani mutum ya kai wa wani malami da makamin karfe a kan titin Roudaki a birnin Tehran tare da tserewarsa a ranar Litinin, mai gabatar da kara na Tehran ya ba da umarnin gudanar da bincike na musamman don gano tare da kama wannan mutumin.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Bayan harin da wani mutum ya kai wa wani malami da makamin karfe a kan titin Roudaki a birnin Tehran tare da tserewarsa a ranar Litinin, mai gabatar da kara na Tehran ya ba da umarnin gudanar da bincike na musamman don gano tare da kama wannan mutumin.

Wanda hakan yasanya bayan gudanar da bincike a daren jiya, an gano wannan mutumin, aka kama shi, aka mika shi ga hukumomin shari’a.