Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

15 Yuni 2023

11:23:20
1373198

An Jikkata Falasdinawa Uku Tare Da Shahadantar Da Daya A Yammacin Gabar Kogin Jordan

Matakin da gwamnatin sahyoniyawan ta dauka na rusa gidan wani fursuna na Palastinawa ya yi sanadiyar mutuwar wani Bafalasdine daya da kuma jikkata wasu uku.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Sojojin Isra'ila sun shiga birnin Nablus da ke gabar yammacin kogin Jordan a ranar Laraba (a daren jiya) don lalata gidan "Usame Tawal", wani fursuna dan kasar Falasdinu wanda yake jami'in dakarun gwagwarmaya ne, inda shigar ta su ta haifar da rikici da Falasdinawan.

A cewar jaridar Yediot Aharonot akalla Bafalasdine daya ya mutu sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin bangarorin biyu, sannan wasu Falasdinawa uku sun jikkata.