Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

15 Yuni 2023

11:14:00
1373196

Ayatullah Ramadani: Yaren Kur'ani Harshe Ne Na Hankali Da Dabi'a

Babban sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya bayyana cewa: Harshen kur'ani harshe ne na hankali da dabi'a, kuma mutane za su iya amfana da shi a kowane zamani.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya nakalto maku cewa, babban magatakardar majalisar duniya ta Ahlul-baiti (AS) ya bayyana cewa: kasashen yammacin duniya suna kokarin sanya tsarin rayuwa na Musulunci wanda ya ginu bisa adalci da ruhi da addini da hankali a kan tafarkin zaman duniya da sassaucin ra'ayi. Idan har ya zamo wani tsari yana da alaƙa da ɗabi'a, al'adu na sassaucin ra'ayi na siyasa to ka'idoji da tushen tsarin za su lalace.


Ayatullah "Reza Ramezani" a yammacin jiya - Laraba 24 ga watan Khurdad 1402 (14/June/2024)- a taron malamai da daliban jami'ar Al-Mustafa Al-Alamiya ta Tabriz ya bayyana cewa: Harshen kur'ani harshe ne na hankali da dabi'a, kuma dukkan zamuna za su iya amfana da shi.


Ya yi ishara da wasu shakku da ra'ayoyi dangane da kur'ani inda yake cewa: A bisa tafsirin wasu malaman addini, Alkur'ani ba littafin shari'a da rayuwa ba ne, sai dai face wani bangare ne na mu'ujizozi da nasiha, sai dai ayoyin da suka shafi gwagwarmaya da jihadi, kuma Qur'ani ba ya aiki a duniyar yau.


Babban Sakatare na Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya kara da cewa: Wasu kuma na ganin cewa Alkur'ani na wani zamani ne na musamman, wasu kuma sun yi amfani da harshen larabci na kur'ani a matsayin uzuri da daukarsa ya kebanta da wani sashe na mutane, mayar da martani ga wadannan mutane, ya kamata a ce harshen Alkur'ani harshen hankali ne kuma na dabi'a kuma mutane za su iya amfana da shi a kowane zamani.


Ayatullah Ramezani ya ci gaba da cewa: Wani bangare na koyarwar kur'ani shi ne tarbiyyantar da dabi'un mutane masu tsarki a dukkan fagage ba wai ga 'yan Shi'a da musulmi kadai ba, ba wai kawai na addinan Ibrahim ba, sai dai zamu iya gabatar da koyarwar Alkur'ani ga dukan mutane.


Da yake bayyana cewa Alkur’ani na dan Adam ne kuma littafi ne da kwafi na bangarori daban-daban na rayuwa, ya ce: A bisa ayoyi da hadisai, aikinmu na farko shi ne fahimtar addini, kuma wajibi ne mu koyi ilimin addini ta hanya mai zurfi, kuma mu yarda muyi imani da shi, mu zamo ma'abota addini.


Babban sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya tunatar da cewa: Wajibi ne a koyi addini daidai ta hanyar data dace cikin zurfafawa ta hakane zamu iya koyar dashi cikakken koyarwa.


Dangane da abin da al'umma ke bukata daga daliban, ya ce: Mutane suna sa ran dalibai su koyi addini da kyau kuma su koyar da shi daidai da kuma cikakkiyar fahimta saboda haka, yana da kyau a kula da tsofaffin sunnoni da al'adun makarantar hauza, kuma wajibi ne a kiyaye da kuma ci gabantar da sunnonin.