Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

10 Yuni 2023

00:40:08
1371911

SHEKH IBRAHIM YA'AQUB ALZAKZAKY: SHEHU DAN FODIYO JAN LAYINMU NE

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ja kunnen masu cin mutunci da aibata Mujaddadin addinin Musulunci a nahiyar nan, Shehu Usman Dan Fodiyo (RA) da cewa, su fahimci cewa Shehu Usman jan-layi ne a wajenmu.


Shaikh Zakzaky, wanda aka haska jawabinsa na rufe taron Makon Dan Fodiyo da dandalin Dalibai na Harkar Musulunci suka shirya a karshen makon da ya gabata a Sakkwato, ya bayyana cewa: “Don mutane su sani, mu fa Shehu Usman Dan Fodiyo a wajenmu shi ne ‘khaddul ahmar’, wato Jan-Layi, shi ne ake ce ma ‘red line’ da Ingilishi.”

Ya jaddada cewa: “Mu Shehu Usman Dan Fodiyo jan layi ne a wajenmu, da zaran ka taba shi to mu ainihin shaksiyyarmu ne kake nema ka rusa gaba daya. ‘Personality’ dinmu kake neman ka rusa gaba daya, kamar kana nema ka nuna babu mu ne ma, ko ba a yi mu ba ma sam-sam. Domin shi ne alamin da ya yi duk cikanmu.”

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, ShaikhZakzaky yace: “Duk cikanmu Dan Fodiyo ne, kuma tinkahonmu Dan Fodiyo ne, saboda haka babu yadda za ka taba Dan Fodiyo ya zama ba ka rusa mu bane. Don haka wani abu ne da ba za mu taba amsa ba. Kuma duk wanda muka ji ya taba Shehu Usman Danfodiyo ko yaya ne, to mun san abin da yake nufi, yana nufin ya rusa mu ne, da asalinmu, da tarihinmu, da komai namu. Yana so ya nuna mana cewa yanzu mu bayi ne, ba mu san komai ba tun fil-azal, yanzu kuma yana neman hanyar da zai zo ya dora mana wani abu ne daban ba addini ba, ba kuma abin da muka gada ba.” 


Ya cigaba da cewa: “Tunda shi Shehu Usman Dan Fodiyo (RA) ya ga yanayi ne da ake zaune a ciki da ya sabawa addinin Musulunci, sai ya yi kira ga addini, addinin kuma ya kafu. To idan wani yanzu ya zo yana neman yace shi wani abu ne daban, to me yake nufi? Zai rusa addini kenan ko? Ya kafa wani abu daban.”


Yace: “Ba mu san ma me yake so ya kafa ba, tunda ba za a sauwala a komar da mu Nasara ba ai ko? Wani bai isa ya malkwaya yace, ai yanzu mun koma Nasara ba. Kuma wani ba zai koma yace ya maishe mu Yahudu ba… To abin da yake nufi ya maishe mu, ko me me yake so ya maishe mu, zai maishe mu bayin wasu ne, ba bayin Allah Ta’ala ba. Wannan kuma ba zai taba yiwuwa ba!”

Shaikh Zakzaky yace: “Na kuma tabbatar har ga Allah, babu wani mutum ko shi wane ne da zaice shi Musulmi ne, kuma yana da’awa da sunan addinin Musulunci, yake magana a kai, yace wai zai taba shaksiyyar Danfodiyo! Ta ina za kayi wannan? Mutumin da yayi kira izuwa ga addini, addini ya kafu, ta ina kai zaka zama Musulmi kuma ka taba shi? Ba dai da sunan addini ba.”


Yace: “Idan kace mana da sunan kai Bahaushe ne, to me kake so ayi? A koma irin abin da ake a kai da can kafin Shehun ya bayyana? Za a koma bori da maita da tsafi ne? Sune za kayi kira gare shi?”


Tun da farko, sai da Shaikh Zakzaky ya fara da bayani a kan yadda addinin Musulunci ya sanya mutane baki daya da dukkan kabilu da bangarorinsu a matsayi daya, inda ya nuna cewa, wani na fin wani ne kawai da gwargwadon tsoron Allah dinsa. Yace, ba wai Hadisi bane, Ayar Alku’ani ne Allah Ta’ala yace da mu: “Wanda yafi a cikinku a wajen Allah Ta’ala shine wanda yafi taqawa.” Yace, ta nan ne ake sanin wanda yafi wani.”

Shaikh Ibraheem Zakzaky ya kuma kawo fadin Manzon Rahma (S) dake cewa: *“Babu bambanci tsakanin Balarabe da Ba’ajame sai da taqawa.”* Don haka yace duk mutane daya suke a wajen Allah, a kokarinsa na nuna rashin muhimmancin fadace-fadace da sunan kabilanci ko abin da yayi kama da shi da wasu ke kokarin haddasawa a tsakanin nan.


Shaikh Zakzaky (H) yayi martani ga wadanda ake amfani dasu da sunan su Hausawa ne zasu yaki Fulani, ko wasu da ake bayyana su a matsayin su Fulani wai zasu yaki Hausawa da cewa: *“yanzu an zo an kitsa mana wani irin gaba, ance wai akwai wasu mutane sunansu Hausawa, akwai wasu mutane sunansu Fulani, wai kuma abokanan gaba ne. Rana tsaka aka akawo mana wannan. Kuma wannan yazo ne a tunanin Bature, ba tunaninmu ba ne.”*

Yace, sarakunan Hausa wadanda suka yaki Shehu, tun a wancan lokacin sune suka yi kokarin nuna Shehu Usman Dan Fodiyo a matsayin Fulani, a maimakon su ambace shi da mai kokarin kira zuwa ga addini. “Maimakon su rika ce ma (Almajiran Shehu) dakarun Jihadi, ko (suce) ga masu kira zuwa ga addini nan, sai suka ce musu Fulani.”

Ya kuma bayyana cewa, ba Shehu Usman ne ya fara yakar sarakuna ba, sune suka yake shi, shi kuma ya kare kansa. Kuma wanene ya yaki wani tsakaninsu da Shehu? Su suka yaki Shehu. Shi Shehu Wa’azi yake yi, yana karantarwa ne yana wa’azi. Sune suka yi tunanin cewa zasu kawar da shi. Kuma ko da suka yi kokarin kawar da shi yayi musu hijira ne, ya gudu ya kyale su, amma suka bishi da yaki.

To a lokacin ne tunda yake sun bullo da abin da yaki ne, shine shi kuma wajen kare kansa, sai Allah Ya dora shi birbishinsu, har Allah Ta’ala ya bashi nasara a kansu daya bayan daya, har aka kafa daula ta Musulunci.

Yace: “In yaso wani ya kira (daular) duk abin da yaga dama, amma Musulunci shine asasinta, shi ne abin da aka kafu a kai, ba Fulatanci ba. Da Fulatanci ne abin ai da sai a ce yanzu an hana magana da wani harshe banda Fulatanci. Ko ba haka bane? Sai ya zama kowa ya narke Hausa ma kawai yake yi tunda yake kasar Hausa ce, kuma dama shine harshen wajen (tun a wancan lokacin).” 

Ya kara da cewa: “Kuma za'a ga duk da yawan rubuce-rubucensu a lokacin sunyi ne da harshen Arabiyya, don shine harshen aiki. Lallai Hausa bata taba zama harshen Hukuma a hukumance ba, harshen magana ce kawai a lokacin, domin duk wasu rubuce-rubuce na aikin hukuma da Arabiyya aka rika yi.”

Shaikh Zakzaky ya jaddada bayanin da ya saba yi a kan cewa a gane Hausa ba kabila bace ballantana a samu wasu mutane suce sune kabilar Hausawa, balle kuma suce zasu yaki wata kabilar.

Yace: “Hausa kasa ce, babu wata Kabila mai suna Hausa. Ita kasar itace Hausan. Duk wadanda suke zaune a wajen su ne Hausa, kuma suna da kabiloli daban-daban, suna da harsuna daban-daban. Harsuna daban-daban a tsakaninsu da shigowar baki daga waje ne, sai wani harshe sabo ya bayyana sunansa Hausa.

“Saboda haka Hausa da farko muna iya cewa kasa ce, sannan kuma suka zama mutanen da ke zaune a wannan kasar, na uku kuma ya zama harshen mutanen kasar, na hudu kuma ya zama al’adun mutanen kasar. Saboda haka su wane ne Hausawa? Hausawa sune mazauna kasar Hausa, masu magana da harshen Hausa, suke da al’adun Hausa. Amma ba kabila bane.”


Ya tambayi masu cewa Hausa kabila ce da cewa: “Su ‘ya’yan wane ne?” Yace: “Ba ‘ya’yan mutum daya bane, sun fito ne daga Gabas da Yamma da Kudu da Arewa. Meya hada su? Zaman wuri daya da harshe daya. Saboda haka su Fulani da suke zaune a kasar Hausa, su ma Hausawa ne? Eh! Nufawa suma Hausawa ne? Eh! Yarbawa ma da suke kasar Hausa Hausawa ne? Eh!” Ya tabbatar.

Ya cigaba da cewa: “Baku ga ma suna da abin da suka kira Hausa bakwai ba? Da kuma wasu bakwai din ba zan kira sunan da suke fada da ba, a dayan bakwan ai sunce har da Nufawa da Yarbawa ko? Da Jikum ma Hausawa ne. Duk wanda suke zaune a kasar Hausa suke magana da Hausa sunansu Hausawa, sawa’un suna da harshe banda Hausa ko basu da shi”.

Ya jaddada cewa: “Wani abu muhimmi wanda kowa dole ya san shi, shi ne, Hausa ba jini bane. Babu jinin Hausa. Jinin Hausa ne babu sam! Domin idan kace min (akwai) jinin Hausa, sai nace ‘ya’yan wanene? Babu wani wanda yace su ‘ya’yan ko Bayajidda ne, (domin) dama akwai kasar Hausa kafin Bayajidda yazo, Bayajidda ya samar da gidan sarauta ne a kasar Hausa.”


Shaikh Zakzaky yace: “Garuruwan da suka fi muhimmanci a lokacin guda bakwai, aka tura jikokinsa (ko yayansa) suka samar da wadannan garuruwan, amma dama akwai garuruwan, ba su suka kafa su ba. Sannan bayan nan kuma wasu garuruwan ma da suka zo suka yi karfi suka zama su ma suna magana da Hausa din ne.”


Yace: “Saboda haka, ba daidai bane wani mutum yace mana wai shi yana da jinin Hausa ba. Babu wani jinin Hausa sam-sam! Babu shi sam-sam.” (Ballantana a yi fadan kabilanci da sunansa).


Jagoran, ya bayyana rikicin da ake kokarin tayarwa a matsayin aikin makiya. Yace: “Wannan bakar gaban da Bature ya shuka (tun bayan da yaci kasar nan da yaki), shine yanzu ya sake dago dashi, yake nema ya haddasa fitina a tsakanin Al’ummar nan da sunan cewa, akwai wasu mutane sunansu Hausawa, akwai wasu mutane sunansu Fulani.


Har ma yanzu akwai wasu sayayyun shafuka da suke surutai, yanzu zamanin internet da sauki ya zama kowa ya zama rediyo da talabijin din kansa, yanzu akwai wasu shafuffuka da suke bayyana, basu da wani aiki sai antaya ashar da jafa’i da cin mutunci, wai su Hausawa ne suna zagin Fulani.


“Ko da yake naga ma wasu, akwai wadanda suke kiran kansu Fulani suma suna zagin Hausawa. Nakan ce to duk cikanku an saka ku ne. Na ga ma a cikin zage-zagen ma har ana hadawa da zagin wasu kabilu banda Fulani din. Nace to duk wadannan abubuwan da suke yi an biya su ne akan suyi, an kuma saka su ne su yin.”

Shaikh Zakzaky yayi nasiha ga duk masu jin cewa akwai wata sabani da ya kamata ta haifar da gaba alhali suna amsa sunan Musulunci, inda ya bayyana Musulunci a matsayin wani abu da ke dinke sabani da husuma.

Ya kawo kissoshin yadda Manzon Allah (S) ya samu kabilun Aus da Hazraj suna fada da junansu shekara da shekaru a Madina, amma da zuwansa da Musulunci ya hada kansu suka dunkule suka zama abu guda. Yace: “Shi addinin Musulunci hada mutane yake yi dama.”

Yace: “Kuma ko lokacin da Shehu Usman ya kafa daula, ba kowa ne ya zama Musulmi ba. Dama can ba ya samu kowa a matsayin Musulmi bane, amma kuma da yawan mutane sanadiyyar daularsa sun Musulunta. Amma wadanda ba su Musulunta din ba ma, ba an tilasta su ne aka ce sai sun zama Musulmi dole ba, amma sun zauna lafiya a wannan daular. Kuma haka nan al’amarin yake ko a lokacin Manzon Rahma (S).”

Jagora yace: “Yanzu ma idan muna maganar (komawa) addini, sai su ce kana nufin kowa zai zama Musulmi ne? Nace, to wa ya ce maka haka nan? Abin da muke cewa, shi addinin Musulunci ne zai yi iko. Shi yana da nizami, shi tsararren abu ne da ba mu muka yi ba, Allah ne ya aiko da shi. Abin da muke cewa kenan.

Kuma idan shi addinin ya kafu to wanda duk yake ciki idan Musulmi ne, zai zama lazim ya yi aiki da addinin Musulunci, idan kuma shi ba Musulmi ba ne, idan ya Musulunta shikenan ya zama daidai da mu, idan ma bai Musulunta yana addinin duk da ya ga dama, zai dai zauna yana da hakki, sauran al’umma suna da hakki.”

Ya kuma amsawa masu cewa kasar ba ta zallan Musulmi bane, inda suke inkarin yiwuwar kafuwar daular Musulunci da cewa: “sai muce, in dai kasa tana nufin cewa mutanen wajen ace kowa (ya zama) Musulmi ne, to bai taba aukuwa ba a tarihi. Ko da daular Musulunci ta kafu ta mamaye duk duniya, ba kowa ya zama Musulmi ba, ba kuma kowa aka tilasta ma ya zama Musulmi ba.

Kuma ko da aka yi daular Shehu Usman Danfodiyo, ba kowa neya zama Musulmi ba, kuma ba a tilastawa kowa ya zama Musulmi ba. Ba a tilastawa wani zama Musulmi. Saboda haka ba yadda za a yi kace mana wai ba zai yiwu a yi Musulunci ba sai idan kowa ya zama Musulmi. (Mu) ba abin da muka ce maka kenan ba.”

Ya cigaba da ba da amsa ga masu cewa ai kasa ba ta Musulmi kadai bace, da cewa: “Kasar ta su waye su kadai? “Da za mu tambaye ku, kasa ta waye? Mu amsa a wajenmu kasa ta Alah ce. Wa ya yi sama da kasa? Wa ya halicci mutane? Wa ya dora mutane a doron kasa? Allah Ta’ala ne. To kasar ta waye kenan? Kasa ta Allah ce. Ba kuma inda Allah Ta’ala ya yanka yace nan wajen na ba masu addini kaza, nan na ba masu addini kaza. Ba inda aka yi haka, kasa ta Allah ce, wanda yace, ‘Shi ne ya ajiye mana kasa sassauka, mu bazu a sassanta daban-daban mu ci arzikinsa.”

Jagora Shaikh Zakzaky ya karkare jawabinsa da nuna yadda makiya addini suka yi kokarin canza ma’anar jihadin Shehu Usman, inda suka yi kokarin nuna ya kafa daular Fulani ne bayan ya ci Hausawa da yaki, a maimakon daular addinin Musulunci. Da yadda suka nunawa mutane kamar Shehu ya bar gadon Sarauta ne, ba na Malunta da addini ba. Wanda ya bayyana wannan a matsayin makamin da makiya suka dauka na haddasa gaba a wannan lokacin.

“Lallai wannan da’awa (ta Harka Islamiyya) tana kokarin ta dawo da martaban da’awar Shehu Usman Dan Fodiyo, a san waye Shehu, me ya aikata? Sannan kuma a cigaba daga inda da’awarsa ta tsaya, ma’ana a cigaba da wannan da’awar har a je bakin ruwa ta Kudu da ta Yamma insha Allahul Azeem, a samu daula kwakkwara da sunan addinin Musulunci, wadda za ta hada al’umman nan gaba daya ta dunkule su karkashin tutar “La’ilaha Illallah, Muhammadur Rasulallah”. Kuma insha Allahu wannan kamar ya auku, don alkawari ne na Allah.” Ya karkare jawabinsa.

Alhmdllh yau muka kawo karshen wannan Rubutu da muka rarrabashi zuwa zango-zango Wanda Wakilolin wannan Gida me Albarka na yada Tafsir da Jawaban Jagoran Shiriya Maulana Allamah Sayyed Zakzaky (H) suka dauki nauyi kawowa.

Shekh Ibrahim Zakzaky H

Wanda Ya Rubuta Maku Isma'il Sani U/Mani