Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

6 Mayu 2023

10:08:57
1363114

Allameh Sajid Naqawi: Ya kamata a kama wadanda suka aikata laifin Parachenar nan take

Allameh Sajid Naqawi shugaban majalisar malaman Shi'a a Pakistan ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa malaman da ba su ji ba ba su gani ba a Parachenar, ya kuma bukaci a kama wadanda suka yi kisan.

Kamfanin dillanci labaran Ahlul-Baiti (AS) -ABNA- ya habarta cewa' A cikin wata sanarwa da ya fitar, yayin da yake yin Allah wadai da wannan aika-aika, ya ce ya yi jimami da alhinin da shahadar malamai, don haka a gaggauta zakulo wadanda suka kisan ta’addanci tare da kama su.


Masana siyasa da masu fafutuka na kungiyoyin Shi'a a Pakistan sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da harin da 'yan ta'addar takfiriyya suka kai a birnin Parachenar, wanda ya yi sanadin mutuwar malamai da dama, tare da yin Allah wadai da laifukan takfiriyya, musamman yunkurin kawo cikas ga hadin kai a wannan kasa.