Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

30 Afirilu 2023

14:50:43
1361589

Kafa Hotunan Kwamandojin Nasara A Filin Jirgin Sama Da Titunan Bagadaza

Kungiyar Popular Mobilisation Organisation (Hashdush Sha'abi) ta sanar da cewa, an sanya hotunan da ke filin jirgin sama da sauran titunan birnin Bagadaza a wadannan wurare tare da cikakken hadin kai da amincewar gwamnati.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahl al-Bait (A.S) ya habarta cewa, kungiyar masu gwagwarmaya ta kasar Iraki (Hashdush Sha'abi) ta fitar da wata sanarwa a jiya Asabar, inda ta sanar da cewa, an dora hotunan shahidai "Abu Mahdi Al-Muhandis da Haj Qassem Soleimani" a filin tashi da saukar jiragen sama da kuma kan tashar jiragen ruwa da titunan Bagadaza sun kasance tare da amincewar gwamnatin Iraki da kuma karamar hukumar Bagadaza.


Kungiyar Popular Mobilisation Organisation (Hashdush Sha'abi) a cikin wata sanarwa da ta fitar ta fitar da sanarwar cewa, abin da ake fada a wasu kafafen sada zumunta na yanar gizo game da sanya hotunan shahidan "Abu Mahdi Al-Muhandis da Qassem Soleimani" a kan hanyar tashar jirgin ba shi da tushe balle makama, kuma hotunan da suke cewa suna a filin jirgin sama da sauran titunan birnin Bagadaza, an sanya su a wadannan wurare tare da cikakken hadin kai da amincewar gwamnati, kuma duk wuraren da aka ajiye hotunan an yi musu rajista a hukumance a karamar hukumar Bagadaza.


................................