Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

30 Afirilu 2023

14:41:49
1361588

Netanyahu: Ba Za Mu Bar Iran Ta Ritsa Da Mu Ba

Firaministan yahudawan sahyoniya ya yi nuni da cewa yana da niyyar aiwatar da wani sabon shiri na kara tabbatar da tsaro a yankunan Falasdinawa da ta mamaye, ya yin da yai ikirarin cewa wannan gwamnatin ba za ta bari Iran ta share su ba.

Kamar yadda kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (A.S) - ABNA - ya fitar da rahoton cewa; Benyamin Netanyahu firaministan gwamnatin Sahayoniya a yau (Lahadi) ya maimaita kalamansa na kin jinin Iran a taron majalisar ministocin wannan gwamnatin.


A cewar rahoton jaridar "Maariu" ta yahudawan sahyuniya, firaministan gwamnatin sahyoniyawan ya yi ikirarin cewa: "Ba za mu bari Iran ta ritsa da mu da ta'addanci ta ko'ina ba. Za mu yi tir da ta'addancin da suke yi da rassa da jigogin kasar nan a yankin.


A wani bangare kuma, Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa wannan gwamnati na da niyyar kafa wata kungiya mai suna "Masu tsaron kasa", wadda aikinta zai kasance na kare mazauna yankunan Larabawa.


Ya yi wadannan maganganu ne bayan ci gaba da ayyukan neman shahada a yankunan Palastinawa da aka mamaye. Yankunan Palasdinawa da aka mamaye sun sha gudanar da ayyukan shahada da dama a cikin watannin da suka gabata, musamman bayan dada daukar matakan yaki da gwamnatin sahyoniyawan tayi.


Netanyahu ya kuma ambaci shirin sake fasalin shari'a a wannan gwamnati mai cike da cece-kuce inda ya ce: "Na yi imanin za a iya cimma matsaya da za ta gamsar da kowa."


Shirin yin garambawul ga tsarin shari'a da majalisar ministocin gwamnatin yahudawan sahyoniya ta gabatar yana fuskantar kakkausar suka daga kungiyoyi daban-daban na yankunan Palasdinawa da ta mamaye. Dubun dubatar mazauna yankunan da aka mamaye sun gudanar da zanga-zanga a fadin kasar sama da makwanni 15 a jere don nuna adawa da wannan shiri.


Firaministan gwamnatin sahyoniyawan da ke fuskantar shari'a na shirin yin amfani da wannan shiri don kaucewa shari'ar da kuma tuhumar da ake yi masa.


........................