Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

23 Afirilu 2023

02:26:58
1359721

Jagora: Ya Kamata Shugabannin Duniyar Muusulmi Su Mai Da Hankali Wajen Karfafa Masu Gwagwarmaya A Palastinu

Jagoran juyin juya halin Musulunci: Ya Kamata Shugabannin Duniyar Muusulmi Su Mai Da Hankali Wajen Karfafa Masu Gwagwarmaya A Palastinu

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce: Ya kamata Shugaban nin duniyar musulmi a yau su mai da hankali kan taimako da karfafa wadanda da suke gwagwarmaya a cikin Palastinu.


Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) ABNA ya kawo maku bayan jagoran juyin juya halin Musulunci da yayi ajiya Asabar kafin Azuhur ga wasu gungun jama'a da jami'ai da wakilan kasashe da jakadun kasashen musulmi, Jagoran ya kira hadin kan a matsayin bukatar gaggawa da kuma muhimmancin da al'ummar musulmi suke da shi, da kuma ishara da irin koma baya da gushewa da gwamnatin sahyoniyawa ta ke yi da kuma rage karfin da take da shi a fili, inda ce: Wannan muhimmin ci gaba ya samu ne sakamakon gwagwarmaya da tsayin daka da al'ummar da matasan Palastinu, a yau. ya kamata shugabannin kasashen musulmi su mai da hankali wajen taimakawa da karfafa wadanda suke gwagwarmaya a cikin kasar Falasdinu.


Ayatullah Khamenei ya bayyana watan Ramadan a matsayin tushen kusantar da zukatan musulmi, ya kuma kara da cewa: Kamata ya yi jami'an kasashen musulmi su yi amfani da wannan damar wajen samar da hadin kan al'ummar musulmi da ragewa da warware sabanin da ke tsakaninsu.


Haka nan kuma yayin da yake ishara da matsalolin kasashen musulmi da suka hada da yaki da tashe-tashen hankula da rashin dogaro da kai da fatara da rashin ci gaban ilimi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Idan har aka bi umurnin kur'ani mai tsarki na "hadin kai akan igiyar Ubangiji" to duniyar Musulunci dake da yawan al'ummar kusan biliyan biyu da ta mallaki mafi mahimmancin wuraren yankin duniya na iya ɗaukar mataki don magance matsalolinta da kanta.


Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya dauki lamarin Palastinu a matsayin daya daga cikin batutuwan da suka fi muhimmanci a duniyar Musulunci, yana mai ishara da koma bayan gwamnatin 'yan mamaya sannu a hankali ya kara da cewa: Wannan koma baya da ya faro a 'yan shekarun da suka gabata, a halin yanzu yana kara habaka, sannan kuma ya ci gaba da samun tawaya. Wanda ya kamata kasashen musulmi su yi amfani da wannan babbar dama.


Ya yi ishara da batun Palastinu da cewa ba wai na Musulunci kadai ba, har ma na dan Adam ne, sannan kuma ya yi ishara da tarukan ranar Kudus da jerin gwano a kasashen da ba na Musulunci ba, ya ce: Tarukan adawa da sahyoniyawan a ranar Kudus da ake yi a Amurka da kasashen Turai, ya samo asali ne sakamakon karuwar bayyanar laifuffukan 'yan sahayoniyawa masu kwace ne.


Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Kasantuwar da dama daga cikin al'ummar Turai wajen goyon bayan al'ummar Palastinu yana da matukar muhimmanci, haka ma a kasashen da suka dogara da sahyoniyawan.


Haka nan kuma ya kira babban abin da ya haifar da wannan mummunan yanayi na gwamnatin 'yan cin zarafi ta Yahudawa da tsayin dakan yan gwagwarmaya mai albarka na cikin gida na al'ummar Palastinu da kuma sadaukarwar da matasanta suke yi tare da jaddada cewa: halin da ake ciki a yankunan da aka mamaye ya tabbatar da cewa al'ummar Palastinu sun kara tsayin daka da gwagwarmaya a fagage daban-daban, gwamnatin karya za taci gaba da yin rauni.


Ayatullah Khamenei ya yi nuni da cewa matakin gushewar gwamnatin sahyoniyawan ya zo karshe yana mai cewa: Shekaru da dama da suka gabata Ben Gurin daya daga cikin wadanda suka kafa gwamnatin karyar ya ce a duk lokacin da muka kare kanmu to za a ruguza mu, kuma za a halaka mu. a yanzu duniya ta shaida wannan lamari, kuma idan wani abu ya faru, kada ku damu, an kusa kawo karshen gwamnatin 'yan mamaya, wanda kuma yana daya daga cikin albarkokin matasan Palastinawa masu gwagwarmaya a yammacin gabar kogin Jordan da sauran yankunan da aka mamaye.


Bisa la'akari da wadannan hujjoji, ya dauki taimako ga dakarun cikin Palastinu a matsayin dabarar da ya wajaba a duniyar musulmi a yau, ya kuma kara da cewa: daidai da irin kokarin da suke da shi mai daraja, fagen gwagwarmaya da dukkanin kasashen musulmi ya kamata su mai da hankali kan karfafa bangarorin gwagwarmayar cikin Palastinu.


A yayin da yake bayyana wani muhimmin batu, Ayatullah Khamenei ya bayyana karkata zuwa ga Musulunci a matsayin babban abin da ke cikin gwagwarmayar kungiyoyin Palastinawa, ya kuma kara da cewa: A lokacin da ba bu karkata ga dabi'un Musulunci, ba a samu wadannan abubuwan ba.


Jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauki matakin adawa da Musulunci na makiya a matsayin sakamako na fahimtar irin karfin da Musulunci yake da shi wajen karfafa al'ummar Palastinu da sauran al'ummomi inda ya ce: Tabbas da yardar Allah da kuma taka tsan-tsan na al'ummar musulmi dabarar makiyan ba za ta je ko'ina ba.


Ayatullah Khamenei kuma yayin da yake ishara da jigo Imam Khumaini (R.A) da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen goyon bayan al'ummar Palastinu, ya kara da cewa: Wannan yunkuri zai ci gaba, muna fatan al'ummar Iran abin kauna za su shaida ranar da musulmin dukkanin kasashen musulmi za su yi salla da yardar Allah a cikin Mai Tsarki.


A farkon wannan taro, shugaba Hujjatul-Islam Islam Wal-Muslimeen Raisi, yayin da yake ishara da irin yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da muhimmanci ga hadin kan dakaru uku, ya ce: Ina tabbatar wa Jagoran juyin juya halin Musulunci da al'ummar Iran abin kauna. cewa dukkanin rundunonin guda uku za su nisanci rarrabuwa da wariya kuma zasu mayar da hankali tare da tausayawa juna da hadin kai a kan tabbataccen batun wanda yake cikin taken shekara da warware matsalolin rayuwar mutane da yi musu hidima da gaske.