Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

18 Afirilu 2023

08:09:17
1359031

Falasdinawa 280,000 ne suka yi tururuwa zuwa birnin Al-Aqsa a daren ranar 27 ga watan Ramadan suna masu nuna goyon bayansu ga Gwagwarmaya.

Majiyar birnin Kudus ta bayyana cewa kimanin masu ibada 280,000 ne ke gudanar da raya daren ashirin da bakwai na watan Ramadan a masallacin Al-Aqsa mai albarka .

Kamfanin dillancin labaran Ahlul Bait As ABNA ya habarta cewa, dubun dubatar Falasdinawa ne suka yi tururuwa a jiya, Litinin, zuwa harabar masallacin Al-Aqsa mai albarka, gabanin I'itikafin daren ashirin da bakwai ga Ramadan. 


Dubban mutane ne suka je shingen bincike na Qalandia, domin isa masallacin Al-Aqsa da kuma raya daren ashirin da bakwai ga watan Ramadan, yayin da wasu sabbin gungun Palastinawa suka isa birnin Al-Aqsa domin sake raya shi a wannan dare mai albarka.


Dubban masu ibada da keɓe kansu wajen ibada sun yi ta rera waƙen nuna goyon baya ga Gwagwarmaya.


Majiyoyin Kudus sun bayyana cewa kimanin masallata 280,000 ne suka gudanar da raya daren ashirin da bakwai na watan Ramadan a masallacin Al-Aqsa mai albarka.


Bayanai sun ce dubban mutane ne suka je shingayen binciken ababen hawa da ke kan hanyar shiga birnin Kudus da aka mamaye, domin isa masallacin Al-Aqsa da kuma gudanar da ayyukan daren ashirin da bakwai na watan Ramadan, wanda ake kyautata zaton daren lailatul kadari ne.


Wani abin lura shi ne cewa, tantuna da dama da 'yan gudun hijirar suka kafa sun bazu a cikin masallacin, yayin da sojojin mamaya suka kara karfi a kofar Al-Aqsa da kuma shingayen binciken ababen hawa na birnin Kudus.


Wani yanayi na imani da ya cika masallata a masallacin Al-Aqsa, a shirye-shiryen gudanar da raya daren 27 ga watan Ramadan, yayin da sojojin mamayar suka karfafa tabbatuwarsu akan tafarkin Mujahidai na masu Ibada dake tsakanin kofar Hatta da Al-Asbat don hana wadanda ke ibada cin abinci sha ruwa.


Daraktan masallacin Al-Aqsa mai albarka, Sheikh Umar Al-kiswani, ya duba yadda ake gudanar da tarbar masu ibadar da suke zuwa masallacin Aqsa mai albarka, domin raya daren ashirin da bakwai ga watan Ramadan.


Kuma ana ci gaba da yin kiraye-kirayen ci gaba da gudanar da tattaki zuwa masallacin Al-Aqsa mai albarka, da kuma kara kaimi wajen gudanar da ibada da i’itikafi a sauran kwanaki na watan Ramadan, tare da yalwar wuraren ibada.

.........................