Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

14 Afirilu 2023

12:40:37
1357950

Bayanin rufe tattakin ranar Qudus yana gargadin yahudawan sahyoniya kan aikata duk wani wauta ga masallacin Al-Aqsa.

Mahalarta muzaharar sun yi tir da mummunan harin da aka kai wa masu Iitikafi a masallacin Al-Aqsa, wanda ya yi sanadin shahada da raunata wasu gungun masu azumi a alkiblar farko ta musulmi da yammacin kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul Bait (As) ABNA ya habarta cewa, mahalarta muzaharar ranar Qudus ta duniya a birnin Tehran sun tabbatar da cewa duk wani wautar da aka yi wa masallacin Al-Aqsa, to za'a biya hakan da abu mai tsada awajen yahudawan sahyoniya, kuma idan har yaki ya barke zai karasa rugujewa masu mamaya ne gaba daya.

Mahalarta muzaharar sun yi Allah wadai da mummunan harin da aka kai wa masu Ibada a masallacin Al-Aqsa, wanda ya kai ga shahada da raunata wasu gungun masu azumi a alkiblar farko ta musulmi da yankin yammacin gabar kogin Jordan a lokaci guda, tare da bayyana goyon bayan tabbatar da mayar da martanin makami mai linzami daga kungiyoyin gwagwarmaya da isar da sakon "hadin kai na gaba" tare da yin gargadin cewa, ko wace irin wauta ce ga masallacin Al-Aqsa da yahudawan sahyoniya za su aikata za su biya hakan da bau mai tsada, kuma idan yaki ya barke to zai kara kaimi wajen aiwatar da ayyukan rugujewa da lalata mahallin masu mamaya.

Sanarwar ta kuma yi Allah wadai da shuru da nuna halin ko-in-kula da tarukan kasa da kasa da cibiyoyin kare hakkin bil'adama suke yi dangane da munanan laifuka da yahudawan sahyoniya suke aikatawa, tare da yin kira ga MDD da ta dakatar da zama mamba tare da korar 'yan sahayoniya masu cin zarafi da wariyar launin fata da kashe yara daga wannan kungiya da sauran su.

An kaddamar da tarukan ranar Qudus ta duniya a Tehran babban birnin kasar Iran da ma sauran garuruwan kasar Iran, tare da halartar dimbin al'ummar kasar domin zagayowar ranar Qudus ta duniya.

Mahalarta muzaharar sun daga tutocin Falasdinawa da tutoci na yabon al'ummar Palastinu, suna masu kira ga al'ummar Palasdinu da nuna goyan bayansu, da kuma yin tir da laifukan sahyoniyawan.

Zanga-zangar dai ta nufi wuraren da ake gudanar da Sallar Juma'a, inda za a gudanar da tarukan ranar Qudus ta duniya, wanda ya kunshi jawabai na wasu 'yan siyasa da kuma fitar da sanarwa a madadin al'ummar kasar

Iran da kasashen musulmi da ma sauran kasashen duniya ne suka gudanar da tarukan wannan rana tun bayan da marigayi Imam Khumaini ya kafa shi a shekara ta 1979, lokacin da Jagoran ya yi kira da a ayyana ranar Juma'ar karshe na watan Ramadan mai albarka a kowace shekara a matsayin ranar Kudus ta duniya.

.................